Addini

Matsayar Addini Akan Gyaran Farce

Addinin musulunci ta koyar da tsafta wanda ya kasance daya daga cikin ginshikin Imani. A ko da yaushe Ana bukatar musulmi ya kasance cikin tsafta ko da kuwa dan ibada ne.

Yanke farce na hanu da kafafuwa Suna matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam. Haka tsaftace jiki yana da amfani wajen kare lafiyan mutum.

Akwai Lokuta da yanayi da wanda zai hana yanke farce?

Addinin musulunci ta zo da matsaya akan haramcin yanke farce, lokutan da ba a hallata gyaran farce ba sun hada da lokacin Umrah da hajji. Dan ko aske gashi bata halatta ba lokacin hajji da umrah.

Bayan Haka, babu wani lokaci da ya haramci mutum ya yanke farce. Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam yace “tsafta yana daga cikin ginshiki na imani” Bukhari ya rawaito.

Tsafta ya samu wuri mai muhimmanci a Addini, wanda hakan yasa gyaran farce da sauransu suke da muhimmanci.

Ya haramta a yanke farce da daddare?

Duk da dai Mun san cewa yanke faratu yafi kyau da rana saboda haske wajen iya gani da Kyau dan kar mutum yayi wa kansa rauni wajen gyara wa da reza ko Aska. Amma babu wani babi na hidisi ko ayah a Qur’ani da tazo da haramcin yankan farce da daddare.

Babu wani lokaci kayyadadde wanda aka bayyana cewa ya haramta a gyara farce ko da rana ko da daddare.

A Duk yanayin da mutum ya samu na nutsuwa Kuma ya lura da cewa farcen sa sunyi girma ko datti. Ana so kayi gaggawan yanke su.

Wace rana ne aka haramta yanke farce?

Malamai da yawa sun tsaya akan muhimmancin yanke farce a safiyar ranar Jumma’a. Tsaftace jiki ranar jumma’a Tana da falala. Amma babu wata kayyadadden rana guda wanda aka haramta gyaran farsuna.

Ranar Jumma’a ta kasance rana ne Mai falala, Ana so Duk musulmi ya zamto cikin tsafta, gyaran farce da aske gashi yana da muhimmanci dan samun lada ranar jumma’a.

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance mai aski da gyaran gashi kamin yayi alwala ranar jumma’a. Annabi yana yin wankan janaba ya Kuma sanya kaya masu kyau da turare kamin ya fita masallaci da wuri ranar jumma’a wanda hakan Maluma sun samu matsaya cewa hakan kamar kayi sadaka ne da rakumi.

Hakan shi ya nuna muhimmancin yanka farce da Kuma tsafta ranar jumma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button