Addini

Hukuncin Sallar Kasaru Da Hada Sallah Na Dr Mansur Isa Yelwa

Hukuncin Sallar Kasaru Da Hada Sallah Na Dr Mansur Isa Yelwa

Hada sallah da yin kasaru ya Shafi ma tafiyi, ko matafiyin da yake kan hanya ko wanda ya isa garin da zaije. Amma yana matsayin bako a inda yaje. Yana iya hada sallah Yana iya kasaru. Amma idan garin da zaka dawo ne na garinku ka iso to ba kasaru kuma ba hada sallah.

Idan zakaje gari mai tsawon tafiyar kilomita dari toh zaka iya hada sallah ta azahar da la’asar, ko da bayan nan ka isa kamin sallar la’asar to inka isa garin sai la’asar tayi to su ta shafa banda kai.

Amma idan kana dawowa ne bakayi sallah a hanya ba ka dawo gida to babu kasaru akan ka, Azahar raka’a hudu la’asar hudu zaka yi. Tunda ka riga da ka iso garinku. Yin kasaru da hada sallah na matafiyi ne.

DOWNLOAD MP3

Amma in ka Isa garin da zakaje bakwanta kana da daman hada sallah da yin kasaru. Amma idan kaje zama ne, misali ka samu transfer a wajen aiki, ko kaje makaranta ko Bautar kasa ta NYSC to kaje zama ne babu kasaru akan ka.

In kaje kwangila ba kaje zama bane zaka yi kasaru Saboda za a iya daga ka kowani lokaci ko ka gama aikin cikin kankanin lokaci. Duk wanda kasaru ta hau kan shi hada sallah ma ta hau kan shi. Mazhabar hanafiyya da na shafi’iyya sun hadu akan kasaru da hada sallah akan matafiyi. Kuma duk zaka iya hada sallah In kana kan hanya muddin ka isa kuma zakayi kasaru babu hada sallah.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button