Biography

Cikakken Tarihin Engr Abdullahi A. Sule, Rayuwarsa, Karatunsa, Aikinsa, Siyasarsa, Gudumawarsa, Iyalansa, Hutunansa

Cikakken Tarihin Engr Abdullahi A. Sule 

Shafin labaranyau.com ta kawo cikakken bayani kan Tarihin rayuwa, aiki da Siyasar A.A Sule gwamna a jihar nasarawa.

Cikakken Tarihin Engr Abdullahi A. Sule 
Cikakken Tarihin Engr Abdullahi A. Sule

Rayuwar A.A Sule

Injiniya Abdullahi A Sule, an haifeshi ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 1959 a garin gudi na karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawan Najeriya. Ya girma a waje mai banbance banbancen addini da qabila. Mahaifinshi Alhaji Sule ya kasance hakimi kuma kakan shi Abdullahi Angulu shine dakacin farko na Kauyen Gudi.

Mahaifiyar sa Hajiya hauwa ta taso a garin Bokono da keffi na jihar Nasarawa.

DOWNLOAD MP3

Karatun A.A Sule

Karatun A.A Sule 
Karatun A.A Sule

Injiniya ya fara karatun Firamare ne makarantar Roman Catholic Mission RCM na garin Gudi Station a shekarar 1968. Bayan ya ci jarabawar gamawa na firamare ya wuce Zhang Commercial school na bukuru garin Jos a shekarar 1974.  A shekarar 1977 ya shiga polytechnic na jihar Filato bayan nan ya samu tallafin karatu zuwa jami’ar jihar Indiana a kasar Amurka a shekarar 1980 inda yayi digirinsa na farko da na biyu cikin shekaru hudu da yayi wajen jajircewa da kuma hazaka da kuma taimakon Allah suka ya kammala a shekarar 1984 inda ya karanci mechanical technology da industrial technology a wannan jami’ar.

Aikin A.A Sule

Aikin A.A Sule

Injiniya ya fara aiki ne tun bayan kammala karatun diploma a polytechnic a shekarar 1980, inda yasamu aiki da Plateau electricity Corporation, a garin Jos. Bayan tafiyar shi Amurka da ya dawo yayi bautar kasa a wannan kampanin. Bayan nan ya samu aiki da jos steel Rolling company ltd, a shekarar 1987 ya samu karin girma zuwa matakin GL 12 daga daga GL 09 Saboda hazaka da iya aiki. Ya bar wannan aikin jos steel Rolling company ltd a shekarar 1989 inda ya koma Amurka a matsayin sa principal production engineer.

Bayan Injiniya Sule ya koma Amurka garin Texas( San Anthonio kamin ya koma Houston) inda yayi aiki da kampanoni kamar su Lancer corporation, san Anthonio OEM components, Houston Houston
engineer, Houston Morgan performance, Houston Dril-Quip incorporated, Houston Osyka corporation duka a Texas.

DOWNLOAD ZIP

Yayi aiki a matsayi daban daban fara da workshop engineer computer Numerical control (CNC) programmer, CNC operator, Facilities Engineer, project/ production engineer da kuma darakta na business development na Afirka da Middle East na Osyka corporation.

Injiniya ya dawo najeriya a shekarar 2000, inda shi da wasu abokansa suka bude kampanin mai me suna Sadiq Petroleum Nigeria Ltd a Jihar legas kuma ya Riqe muqamin MD/CEO.

Sadiq Petroleum ta siya gidan mai na AP African Petroleum PLC. A Sadiq Petroleum suka siya kashi 30 na Kampanin AP. An zabi Injiniya a matsayin Executive Darakta na operation na AP a watan Nowamba 2000. Ran biyu ga watan afrailu shekarar 2001. A matsayin sa Na MD na Hudu a kampanin.

Ya samu kampanin da tarin bashi kamin nan shi da abokan aikinsa suka kawo canji da cigaba. Kamin ya ajiye aiki a shekarar 2006, sai da ya goge bashin Miliyan Ashirin da biyu ya kuma bunkasa kasuwancin ya bar Biliyan Shida a account din kampani.

Bayan ajiye aiki Injiniya Sule ya samu aiki da wani kampanin mai a amurka mai suna tetra a watan juli na shekarar 2006a matsayin darakta na business development/ manajan kasa. Ya kuma bar kampanin Tetra a Disamba shekarar 2006. Domin shiga Siyasar jihar Nasarawa . Bayan bayan barin Kampanin AP ya riqe muqamin darakta a IMB international Bank. Ulti-Care Pharmaceutical da Chrismatel Holdings kuma ya riqe muqamin ciyaman na AP Oilfield Service LTD da kuma star-AP oilfield services.

Gudumawar A.A Sule

Gudumawar A.A Sule 
Gudumawar A.A Sule

Bayan dawowarsa najeriya a shekarar 2000, Injiniya A.A Sule ya yi aikin kansa da na gwamnati wa mutane a jihar Nasarawa. Ya gayyato mutane daga kasashen duniya domin su zo su duba abinda jihar ta ke dashi don saka hannun jari.

Ya yi aiki shi kadansa wajen gyara makarantu da asibitoci, wajajen bauta, security posts, har zuwa lokacin da ya zama mai rikon kwarya janar manajan darakta na kampanin sugar Dangote a legas.

Iyalen A A Sule

Iyalen A A Sule
Iyalen A A Sule

Injiniya Yana da mata biyu da yara, cikin matan akwai Silifa Sule da farida Sule.

Siyasar A.A Sule

Siyasar A.A Sule
Siyasar A.A Sule

Injiniya A A Sule yayi takarar gwamna a jam’iyar APC a shekarar 2019 inda ya lashe zaben ya zama gwamna a jihar Nasarawa.

Ya kuma kara yin takarar gwamna a shekarar 2023 ya sake lashe zaben, domin a yanzu shine gwamna a jihar Nasarawa bayan ya doke David Ombugadu na jam’iyar PDP.

Hotunan A A Sule

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button