Biography

Cikakken Tarihin Sheikh Kabiru Gombe, Rayuwarsa, Aikinsa, Musuluncinsa, Siyasarsa, Karatunsa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Sheikh Kabiru Gombe 

Kabir Muhammad Haruna wanda aka fi sani da Kabiru Gombe, Dan najeriya ne malami kuma mai da’awa, wanda a Yanzu haka shi ne National sakatare janar na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa iqamatus Sunnah daya daga cikin kungiyoyin da suke tafiyar salafiyyah a najeriya tun Disamba 2011.

Cikakken Tarihin Sheikh Kabiru Gombe 
Cikakken Tarihin Sheikh Kabiru Gombe

Rayuwar Kabiru Gombe

An haifi Sheikh Kabiru Haruna Gombe, a garin Kuri a karamar hukumar Yamaltu Deba na  jihar Gombe.

yayi makarantar firamare a garin Gombe, a wata islamiyya ta Izala anan garin Gombe. Sheik Kabiru Haruna Gombe ya samu haddar Al’qurani mai girma tare da gyara karatun sa a wajen maluma irin su:

  • Sheik Zarma Gombe,
  • Sheik Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.

Kuma ya zama Alaramma mai Jan baki tun Yana dan kankanin shekaru a duniya. A hakan Malam ya juya ya koma Da’awah kuma da’awarsa ta shiga lungu da sako na kasar najeriya da wasu kasashen duniya. Ya samu ilimi mai yawa na karatun addini a wajen Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe. Malam ya kasance dan kasuwa ne.

Aikin Kabiru Gombe

Aikin Kabiru Gombe 
Aikin Kabiru Gombe

Kabir Muhammad Haruna ya fara ne da zama dan agajin kungiyar Izala a fannin First Aid. Daga nan sai ya tafi saudiyya inda ya koma makaranta ya karanta Kimiyar Qur’ani, kabiru Gombe ya kasance national sakatare na Kungiyar JIBWIS tun watan Disamba shekarar 2011.

Yana karatun tafsiri kowata shekara in ramadan ya zagayo, garuruwa da kasashen da ya ke tafsiri sun hada da: kano, Abuja, Cameroon, Niger, Chad, Ghana, United Kingdom da sauransu. Kabiru Gombe yana yawan jawo kunne wa mata a gidan aure a wa’Azin sa.

Musuluncin Kabiru Gombe

Musuluncin Kabiru Gombe 
Musuluncin Kabiru Gombe

Muhammad kabir Haruna ya kasance ahlussunnah salafiyya ne, wanda aka sanshi da wa’azi dan wayar dakai kan bidi’ah da rashin ingancin ta a najeriya. Inda ya tsaya da kafafun sa domin bayyana korafin darika da shi’a.

Siyasar Kabiru Gombe

Siyasar Kabiru Gombe 
Siyasar Kabiru Gombe

Kabiru Gombe da Ahmad Sulaiman sun goyi bayan Abdullahi Umar Ganduje akan Jam’iyar PDP a zaben da ta gabata na shekarar 2019 a jihar kano, a cewar su Ganduje ya musuluntar da arna dayawa zuwa musulunci. A lokacin da ake zargin Izala tana karban kudin yaki da boko Haram wanda suka karba a mulkin Goodluck Jonathan a hannun Sambo Dasuki. Muhammad kabir Gombe ya fito ya karyata cewa kungiyar Izala bata karbi komai ba na kudi ko kudin makamai a hannun gwamnati.

Karatun Kabiru Gombe

Hotunan Sheikh Kabiru Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button