AddiniLabaran Yau

Abu Dari Da Ake So Duk Musulmi Yayi Bayan Sallar Asuba

Abu Dari Da Ake So Duk Musulmi Yayi Bayan Sallar Asuba

Manzon Allah in Akayi Sallar Asuba, in ya zauna a wurin baya Tashi Sai Rana ta fito. Yana ta zikiri Kuma yace Duk mai yin haka bare tabe ba. In anyi sallar asuba shikenan ka zauna, Akwai abu dari daya ce kayi.

Kace “Laa ilaha ilallah wahdahu laa sha rika lahu, Lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa alaa kulli shai’in qadeer “

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ‏

Kayi kafa dari.

In kayi haka Allah zai baka lada dari, Allah zai yafe maka zunubi dari, Allah zai daukaka ka daraja dari. Ranan ba wanda ya kaika, Sai wanda ya yi irin wannan ya Kuma kara da abinda ya wuce ka.

Sannan kace “bismillahil ladhi layadhurru ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wa huwas sami’ul Aleem”

بِسْمِ اللهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

Kayi kafa uku, Allah zai kare ka daga sharrin mutum da Aljani.

Kace “Hasbiyallahu laa ilaha illahuwa Alaihi tawakkaltu wa huwa rabbil arshil Azeem”

حسبى الله لا إله إلا هو عليه توكلت وهو رب العرش العظيم

Kayi kafa bakwai.

Kace “Subhanallahi wa bi hamdihi”

سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ kafa dari, za a yafe ma zunubanka ko da ya kai yawan kumfan kogi.

Kace “Astaghfirullahal Azeemal ladhi laa ilaha illahuwal hayyul Qayyum wa’atubu ilaihi”

أسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لا إلَهَ إلا هُوَ الحَيُّ القَيُومُ وَأتُوبُ إلَيهِ

Kayi kafa dari.

Kayi wa Annabi sallati dari:

‏اللهم صل على محمد، وعلى آل محمد كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، اللهم بارك على محمد، وعلى آل محمد كماباركت على إبراهيم، وعلى آل إبراهيم، إنك حميد مجيد

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button