Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Miyar Kuka Cikin Minti Goma

Yadda Ake Miyar Kuka Cikin Minti Goma

Kuka wata bishiyace da take da amfani da muhimmanci ga abinci da magunguna tana kunshe da muhimman sinadarai masu bada kariya ga lafiyar dan adam da suke temakawa wajen magance wasu cututtuka kamarsu tari, ulcer,ciwon koda dama sauransu sinadaran sun kunshi vitamin e, vitamin c, calcium, potassium,da sauransu

Abubuwan da ake bukata

Kuka
Man ja
Attaruhu da tattasai
Albasa
Nama
Daddawa
Wake
Citta
Tafarnuwa
Kanwa
Sinadaran dandano

Yadda ake hadawa

Dafarko zaa daura wake a wuta asaka kanwa kadan da gishiri a barta ta dafu ligif sai a juye ta roba

Sa’annan a maida tukunyar a soya manja da albasa bayan ta soyu a zuba kayan miya wato markadadden attaruhu da tattasai,a wanke nama a zuba,asa daddawa,maggi,citta da tafarnuwa a soyasu tare bayan ya soyu tsaf sai a dauko wakennan da aka dafa tare da ruwan waken ayi sanwa da ita idan ruwan be isa ba a kara daidai yawan da ake bukata sa’annan a saka sinadaran dandano a rufe tukunyar komi ya dafu tsaf ya hada kanshi

Bayan komi yadafu sai a dauko garin kuka a kada miyar da ita daidai kaurin da akeso sai adan diga ruwan kanwa ko ruwan toka a rufe tukunyar ta tafasa idan anaso miyar tadanyi yauki kar a rufe tukunyar miyar kuka ta kammala

Sai a tuka tuwon shinkafa ko gari ya danganta da wanda akeso.

Ga bidiyon yanda ake miyan kuka daga bisani

Yadda Ake Miyar kukan Kaza

Ita miyar kuka da akeyi na kaza ya danganta da irin yadda kike so, amma yau Zan miki yadda zakiyi na kaza mai Dadi.

Kayan Hadi

Kuka
Albasa
Tattasai
Attaruhu
Kanamfari
Citta
Maggi
Gishiri
Kaza

Yadda Ake Hadawa

Da farko zaki yanka naman kazan daidai Yadda kikeson girman naman, Sai ki wanke namar da kyau. Sannan Ki daura a wuta Ki saka ruwa.

Ki wanke kayan miyan Ki Ki markada ko Ki jajjaga ki zuba akai yadda ake farfesu. In kinaso zaki iya saka daddawa kadan ciki har Sai namar ta dahu.

Sai ki zuba kukarki a hankali kina kadawa da bulogari dan kar yayi gudaji.

In yamiki kauri yadda kikeso Sai ki barshi ya dahu kamin Ki sauke.

Akwai Yadda Akeyi Na Tumaturi

Shi Kuma Ana markada kayan miya, Sai a soya kayan miyan kamar yadda ake miyan tumatir (stew) Sai ki zuba maggi da nama Ki kara ruwa kadan, in ya tafasa Sai ki kada kukar ki.

Ba lallai a gane miyar kuka bane saboda dadin da zai miki.

Aci tuwo lafiya.

Yanda Ake Miyan Kubewa

Yanda Ake Miyan Rama

Yanda Ake Miyan Taushe

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button