Girke GirkeLabaran YauTrending Updates

Yadda Ake Miyar Awara (Tofu Soup)

Yadda Ake Miyan Awara

Miyar awara dai an fi yinta a kasashen hausa na fadin najeriya, ita miyar ta kasance daya daga cikin miyar da in an ci ake so a kuma ci saboda ainihin dandano mai gardi da santi da ta ke tatttare acikin ta. cikin kankanin lokaci zaki iya koyar hada wannan miyar.

Kayan Hadi

Waken suya
Manja ko Mangyada
Attaruhu
Tattasai
Albasa
Ganyan shuwaka

Ganyan ogwu

Ganyan albasa
Nama

Bushasshen kifi
Citta
Tafarnuwa
Mosoro
Maggie
Gishiri

Yadda Ake Hadawa

Da farkon Za a wanke  waken suya a rege bayan ancire tsakuwar sannan sai a Kai markade idan aka markada Sai a tace shi da rarriyar tatta a cire dusan  sai a daura tukunya a kan wuta a zuba taceccen ruwan a cikin tukunyan sai a  rufe a barshi ya tafaso sai a zuba manja kadan sbd ya hanashi zuba idan yafara tafasa

Idan ya tafasa sossai sai a Bude a sa ludayi a gauraya saboda kar ya zuba sai a sa masa ruwan tsami na kamu daga nanna ne zai hada kanshi guru guda,to da gannan sai a kwashe shi a Basket ko a Dan kwalin tatta sai a rufe shi a Danne saboda ya tsan tsame

Sai a wanke kayan miyan a jajjaga, sai a daura manja ko man gyada  a soya shi sai a zuba jajjagegen kayan miyan a ciki sai a daka citta,masoro, tafarnuwa a ciki a yi ta soyawa, sai a zuba bushasshen kifi da  Maggie, gishiri a ciki sai a saka taceccen awaran ciki a yi ta soyawa .

Sai a wanke ganyan ogu, shuwaka,ganyan albasa aciki aman kadan ake sakawa ba dayawa ba. Idan kuma da nama a keso a yi amfani to za a dafashi da kayan kamshi sannan sai a zuba a ciki kuma wannan miyan ba a sa mishi ruwa haka ake yin shi da kauri

Yadda Ake Miyar Awara
Yadda Ake Miyar Awara

Ana cin shine da sakwara ko tuwon semovita ko duk irin tuwon da ake so. aci tuwo da miyar awara lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button