Labaran YauFootballForeign

Babu Wanda Ya Cancanci Lamba 9 A Man U Kamarshi: Magoya Baya Nata Korafi

Babu Wanda Ya Cancanci Lamba 9 Ayanzu Kamarshi: Magoya Bayan Man U Nata Korafi

Kungiyar taka leda na Man U ta bayyana Rasmus Hojlund a matsayin sabon Lamba 9 na wannan shashin wasannin 2024. Hakan Ya faru cikin sauki ne daomin kocin Man U ya amince da kokarinsa.

Hojlund yazo kungiyar Man U a shekaran 2023 daga kungiyar kwallon kafa ta Atlanta, wanda ETH ya nuna shaawar samun dan wasan bayan zuwansa Old trafford.

Sabon lamba 9 ya kasance mai kai farmaki ne cikin kwarewa da jajircewa wanda hakan ya bashi daman zura kwallaye sama da goma a kakan bara na wasannin 2023.

Lokacin da yazama zakaran gwaji a tsohon kungiyarsa na Atlanta ya zura kwallaye sama da 30 a cikin wasanni kadan wanda shi ya jayo kasancewarsa zakara a wanan shashin wasa.

Kungiyar Man U ta sanar wa duniya a shafinta na yana gizo, kan cewa zabbaben sabon lamba 9 ta shine. Hakan kuma ya janyo kace nace a tsakanin manyan magoya baya da kuma tsoffin yan wasan kungiyar.

Wasu na cewa kan Joshua Zirkzee, wato sabon dan kai farmaki da kungiyar takawo shine ya can canta a bashi wannan lambar. Gani da cewa tsohuwar lambar Hojlund(11) nada babban tarihi a kungiyar in akayi dubi da irinsu Ryan Giggs da sauransu.

Joshua Zirkzee
Joshua Zirkzee

Hojlund kuma ya ribke da farin ciki ganin burin sa ya cika na samu wannan lamba bugu da kari zuwan Zirkzee ya bashi matukan tsoro dan tunanin rasa lamba wa shi.

Korafi kuma yana dada watsuwa a yanan gizo. Wasu daga cikin magoya baya sun amince da wannan tsari ganin cewa suna da yarda da aminta a irin wasan da Hojlund ke bugawa a matsayin mai kai farmaki.

Wanda har wani babban me goyon baya yake cew a shafinsa, “Lallai wannan zabi yayi matukar kyau, kuma ina da tabbacin Hojlund zaici kwallaye fiye da 30 a wannan shafin wasan”.

Wani Ma ya kara da cewa “Ku kalli fuskan da zata zira kwallaye 40 a wannan shafin wasanni” wanda dayawa sun aminta da bayaninsa gani da yanda suka zubo bayanan burgewa akan dan kwallon.

Amma Hakan bashi ya hana fittar korafi ba, yanda wani ke rubutawa a shafinsa na sada zumunta, yace “Be kamata ayi gaggawan bada lambar nan ba, da an bari Hojlund da Zirkzee sun buga shafin wasanni guda tare anga wanda yafi wani”

Bayan wannan tsari kuma kungiyar ta zayyan cikakken yan wasan ta guda 29 wanda zasu halarci wasan ziyara na wannan shekarar a nahiyar turai wato America.

Yan wasan sun fito dagaske wurin horaswa domin samun cikakkiyar lafiya buga wasannin cikin nasara da kwarewa.

Yan Wasan Man U A Filin Horaswa
Yan Wasan Man U A Filin Horaswa

A Yau 24 ga watar Yuli ne jirgin kungiyar take tashi domin isa kasar amurka don fafatawa da kuma samun nasara. Kadan daga cikin hotunan yan wasan yayin horaswa dakuma tafiya na kasa da fahimtar cikkakkiyar labarin.

Yan Wasan Man U A Jirgin Tafiya Amurka
Yan Wasan Man U A Jirgin Tafiya Amurka

DUKA DUKA KWALLAYEN RASMUS HOJLUND A MAN U 2023

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button