
Advertisements
Yadda Ake kosan Rogo
Ita kosan rogo abinci ne wanda aka fi yin shi a kasar hausa, ita kosar Rogo Ana yin ta da garin kwaki ne. Ga takaicaccan bayani game da kosan rogo saboda bata da wuyan yi.
Kayan Hadi
Advertisements
1:Garin rogo(garin kwaki) Kofi biyu
2: Attaruhu kamar na 50naira
3:Maggie na 50naira
4:onga(stew) guda daya
5:Mangyada Gwangwani daya
6:Albasa na 50naira
Yadda Ake Hadawa
Dafarko zaa tsince baki baki a garin da kuma kasa kasa dake ciki in akwai, sai a juye a turmi asa ruwan zafi kadan a daka haka idan da rogon ne zaayi a yayyanka kanana asa a turmi a daka, har Sai ya kama kanshi yayi laushi.
A jajjaga attaruhu in kanana ne a zuba kamar guda biyar in Manya ne a zuba guda uku depending on irin zafin attaruhun da Albasa shi kuma in manya ne a saka Babba guda daya in kanana ne a saka guda uku , Maggie guda uku ko hudu yadda zai yi miki, Onga stew guda daya ,a zuba Akai a daka sosai yayi Danko.

Sai a kwashe ana dan marawa, kamin nan an saka tukunyar suyar a wuta an zuba mangyadar ta danyi zafi Sai a fara sakawa ana soyawa amai idan ya soyu a kwashe
Ana ci ta garin kuli kuli ko yaji
Advertisements