Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Alale (Moi Moi)

Yadda Ake Alale (Moi Moi)

Ita Alale dai abincin kowa ne a fadin kasar Najeriya har da makwabta. Abinci ne Mai dauke da nau’i na Protein a jikin dan Adam. Cikin sauki ga yadda za a sarrafa Alale.

Kayan Hadi

Wake Gwangwani Hudu
Manja ko mangyada
Maggie guda 8
Gishiri kadan
Kwai guda hudu
Albasa Manya Guda Biyu
Attaruhu  na 50naira
Citta na 50naira
Tattasai na 100naira

Yadda Ake Hadawa

Dafarko za a zuba wake kamar kofi biyu a turmi a surfe,za a sa ruwa kamar rabin kofi saboda ya surfu sossai sai  a juye a wani container a zuba mishi ruwa a wanke har sai ya fita Sossai sai a regeshi saboda kasa ya fita sai kuma a tsince Baki Bakin

Sai a wanke attaruhu,tatasai da albasa a dan daka citta a zuba sai a markada da shi
Zaa Saka daidai yanda ake bukata ne idan anaso yaji yafito sai asa attaruhu sosai

Za a zuba mangyada ko manja kaman gongoni biyu a Kofi hudun da Maggie iya yanda akeso da Kwai kaman guda biyu da gishiri in kina so inki naso zaki iya daka cryfish ki zuba sai a buga shi kamar na kosai kafin sai a sa ruwa saboda yayi laushi cikin bazai yi tauriba da Ruwan zafi za a kwaba kar a zuba ruwan zafin dayawa ba a so yayi ruwa ruwa yadan yi kauri madaidaici sai a zuba a Leda a kulla

Alale
Alale

Ko a shafa manja ko mangyada a gwangwani a Zuba kullin alalen a ciki sai a jera a madambaci a rufe saman da Leda sai a rufe shi kirif a daura a wuta na tsawon minti 40 yadahu sai a sauke.

Moi Moi Alale
Moi Moi Alale

Ana iya dafa hanta ko nama asa acikin kwabin alalen  idan akwai

Za a iya cin shi da yaji ko miya ko Hakan shi.

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button