Labaran YauGirke Girke

Yadda Ake Jollof Na Shinkafa Cikin karamin Lokaci

Yadda Ake Jollof Na Shinkafa Cikin karamin Lokaci

Shinkafa dai a kasar hausa Ana kiranta yar kullum, saboda mafi yawan gidaje cikin hausawa Ana dafa shin kafa kullum. Shinkafa ba abinci ne wanda ake saurin gajiya da ita ba.

Shinkafa Tana da nau’i daban na sarrafa ta, a yau dai zamu kawo miki yadda ake sarrafa Shinkafa wato Jollof. In kin bi yadda muka nuna miki a nan bara aji kunya ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Kayan Hadin Jollof

Shinkafa

Tattasai

Attaruhu

Albasa

Citta

Tafarnuwa

Maggi

Gishiri

Man gyada ko manja

Nama ko kifi

Yadda Ake Hadawa

Da farko zaki saka ruwa a wuta sai yayi zafi sosai sai Ki zuba Shinkafa, in kin zuba sai kulle shi na a kalla minti goma sha biyar, sai Ki sauke ki wanke Ki ajiye a gefe. Dalilin wanke war saboda a rage starch din da yake cikin Shinkafar wanda zai iya mai da shinkafar kamar gwate gwate.

Sannan ki tafasa namanki inda hali in kin wanke namar Ki zuba kayan miya wanda aka jajjaga albasa, tafarnuwa, citta da attaruhu da dan maggi ko onga haka. Sai ki ajiye a gefe.

Sai ki soya manja ko man gyada, Ki zuba jajjagen tattasai dasu albasa da attaruhu da citta da Tafarnuwa. Sai ki soya shi, Ki tsame namar cikin ruwan namar da kika tafasa Ki hada aciki su soyu tare da kayan miyan.

Sannan Ki zuba maggi da gishiri sai Ki juye ruwan namar, in kinaso Ki kara curry da thyme, amma in baki da halin hakan, sai kara ruwa yanda zai karasa dafa miki namar in ruwan namar bare kai ba.

Ki rufe shi ya tafasa kamin ki zuba shinkafar, bayan minti goma sha biyar in akan gas ne na tabbata abincin Ki ya hadu.

Sai ki sauke a zuba aci Jollof din shinkafa mai Dadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button