Labaran Yau

Abbas ya kada Wase da Jaji a a takarar Shugaban Majalisan Tarayya

Abbas ya kada Wase da Jaji a a takarar Shugaban Majalisan Tarayya

Dan Majalisan tarayya mai wakiltar zaria a jihar Kaduna. Tajudeen Abbas ya lashe zaben shugaban cin Majalisan tarayya na 10.

Abbas ya kasance dan so idon jam’iyyar APC yaci da kuri’u 353, ya doke tsohon mataimakin shugaban Majalisan tarayya Ahmed Idris Wase wanda Ya samu Kuri’u 3.

Aminu Jaji shima dan takara ne wanda ya samu kuri’u uku.

DOWNLOAD MP3

Tsohon Jagora na Majalisan tarayya ta 9 Alhassan Ado Doguwa ya yi mubayi’a da Shugabancin Abbas da Nnolim Nnaji na jihar Enugu.

Tijjani Kayode Ismail ya fito da Wase wanda Mohammed Ari Abdulmumin ya mara masa baya.

Haka Ahmed Yusuf Ibrahim ya fito da Aminu Jaji wanda Ahmed Ibrahim ya mara masa baya.

DOWNLOAD ZIP

Anyi zabe da rantsuwan ne a dakin da yan Majalisan tarayya ta tara suke gudanar da Majalisar saboda gyaran da ake a fadar Majalisan tarayyan.

Mataimakin kilakin Kamoru Ogunlana ya bayyana cewa zababbun yan Majalisan tarayya 359 sukayi zabe. Daya dan taraba ya rasu bayan zaben da ta gabata.

Benjamin Okezie Kalu ya zama mataimakin shugaban Majalisan tarayya babu zabe babu yan takaru.

Kalu ya kasance mai magana da yawun Majalisan tarayya ta 9.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button