Labaran Yau

Jami’ar Bayero Ta Kano (BUK) Tayi Rashin Jajircecce Kuma Meh Hazaka…

BUK tayi rashin Jamil Salim

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) Tana Mai sanar da rasuwan rajistaran ta, Jamil Ahmad Salim.

A sanarwan da sa hannun Shugaban jami’ar, Sagir Abbas sukayi, sun bayyana cewa shi marigayi ya rasu ran laraba da Safiya, a garin Kano bayan ciwo na karamin lokaci.

DOWNLOAD MP3

Bayanin sanarwan ta kasance kamar haka, “da bakin ciki jami’ar Bayero take bayyana rasuwan rajistaran ta, Malam Jamilu Ahmad Salim.

“Malam Salim ya kasance rajistara a jami’ar na shekaru hudu wanda an yaba shi da jajircewa da hazaka wajen aiki, hakan yasa yana daga cikin wanda suka kawo ci gaba a jami’ar.

“Jana’izar marigayin an saka za ayi karfe goma na safe a babban masallacin sabon jami’ar Bayero a Kano.

DOWNLOAD ZIP

“Rashin Malam Salim babban rashi ne wa jami’ar BUK da kuma Al’ummar ilimi a Najeriya.

“Anyi rashi wanda bara a manta ba don hazakan sa da aiki tukuru dan samo cigaba da a harkar ilimi a jami’ar”.

Malam salim ya rasu yana mai shekara 60, Kuma an binne shi yanda addini ya tsara, a makabartan dandolo a Kano.

An zabe shi a mai rikon kwarya na rajistara ran 15 ga watan maris a shekarar 2021, bayan nan aka tabbatar dashi a matsayin rajistara A watan Oktoba a wannan shekaran.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button