Yadda Ake Fruit Salad Na Custard Da Madara
Ana yin fruit salad iri iri, yau Mun kawo muku wata nau’i na fruit salad wanda ake yi da custard da madara. Biyomu kadan jin takaicaccen bayani game sarrafa wannan salad mai Dadi.
Kayan Hadi
Lemo
Apple
Ayaba
Inibi
kankana
Duk Wanda ka samu kaman guda biyar ko fiye
Madara
Zuma ko sugar
Yadda Ake Hadawa
Dafarko zaa zuba madara da ruwa a kwano a gauraya kaurin Dan daidai ba tsalalo ba sa’annan a zuba a tukunya ana juyawa ya tafasa
Bayan ya tafasa sai asaka garin custard a kwano asa ruwa a gauraya Shima kar yayi kauri kuma kar yayi tsalalo sai a juye a madaran dake tafasan ana juyawa custard din ba Mai yawa ba saboda baaso yayi kauri kaman kunu sai a saka Zuma ko sugar abarshi yadan huce
Sai ki yayyanka fruits dinki a kwanon da zaki hada sa’annan ki juye wannan madaran custard da kika hada Akai ki dan jujjuya sai ki saka Zuma Akai sai a deba asha.