Cristiano Ronaldo_7 – (1 Billion Followers)
Cristiano Ronaldo_7 yacika mabiya 1 billion a gaba daya shafi sada zumunta, ya mika sakon nuna murnan sa dakuma jin dadin kafa babban tarihi a jigon tarihin duniya.
Ya fitar da sakon ne a shafuffukansa na sada zumunta wanda ya kama da facbook, intagram, X, da kuma sauransu.
Ya nuna murnanshi na tafiyar da kuma goyon bayan da mabiya ke nuna masa a gaba daya tarihin rayuwansa na kwallon kafa.
Yace wannan ya wuci tarihi, ya zama abun alfahari dakuma yin nuni da hadin kai na sauyin tunani da ake nunawa tafiyar sa me tasiri.
Ya kira mabiyan sa da sunan ‘iyali’ inda ya nuna dankon kaunar dayake dashi wa mabiyan nasa. Tafiyarsa yazama canji wa fuskan kwallon kafa kuma yana murna da hakan.
Cristiano Ronaldo_7 yayi bayani kamar haka:
“Mun kafa tarihi – Mabiya BILYAN 1! Wannan ya wuce lamba kawai – shaida ce ga sha’awarmu, tuƙi, da ƙauna ga wasan da bayanta.
Tun daga titunan Madeira zuwa manyan matakai a duniya, koyaushe ina wasa don dangi da ku, kuma yanzu biliyan 1 daga cikinmu muna tare.”
Ya kara dacewa:
“Kun kasance tare da ni kowane mataki na hanya, ta cikin dukkan mafi girma da ƙasƙanci. Wannan tafiya ita ce tafiyarmu, kuma tare, mun nuna cewa babu iyaka ga abin da za mu iya cimma.
Na gode don gaskata yarda da ni, don goyon bayan ku, da kuma kasancewa ɓangare na rayuwata. Mafi kyawun har yanzu yana zuwa, kuma za mu ci gaba da turawa, cin nasara, da kafa tarihi tare.”