Dalibar Computer Science yar aji 300L a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, Naja’atu Salisu, ta rasa ranta bayan ta fadi a bandaki a safiyar Juma’a.
Majiyoyi sun bayyana cewa Naja’atu ta shiga bandaki ne a hostel din dalibai mata dake Gubi campus na ATBU domin yin wanka da safe da kuma shirye-shiryen karatun ta, amma daga baya aka gano ta kwance a sume a falon bandakin.
Rahoto yazo daga cikin abokan zaman Naja’atu, wanda ta bukaci a sakaya sunanta, tace har ta gama aikinta na safe da ta saba ta fito da kayan da ta nufa ta saka zuwa aji, ta bar su a gefen gadonta,
Da ake tabbatar da faruwar lamarin, an ce an garzaya da ita asibitin jami’ar domin kula da lafiyarta, amma jami’an lafiya sun kasa gano wata jijiya a jikinta.
Sannan an kai Naja’atu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwar ta.
A ranar jumu’ar an yi jana’izar Naja’atu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tare da yi mata addu’o’in samun lafiya.