Labaran Yau

Hukumar NAFDAC Ta Haramta Shigowar Indomie A Najeriya

Hukumar NAFDAC ta haramta shigowar indomie a Najeriya

Hukumar kula da Abinci da kwayar Magani ta Nafdac ta hana shigowa da taliyar indomie a kasar Najeriya.

Rahoton ta biyo bayan kasashe kamar taiwan da malaysia sun bayyana illar taliyar wanda ke kunshe da chemical mai suna ethylene Oxide, wanda ke jawo cutar kansa a cikin taliyar.

A jawabin Hukumar Nafdac ranan litinin, darakta janar na Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, Yace Hukumar zatayi bincike kan taliyar da kuma maginta a kampanonin taliyar ran talata.

Jawabin ta bayyana cewa An haramta shigowa da Taliyar indomie a kasar da jimawa.

“Taliyar Tana cikin harmacaccen abinci a jadawalin Hukumar Nafdac, kuma bata da rajista”

“Abunda mukeyi shine Muna kara kula dan shigowar Taliyar. Kuma kara kula da magin indomie da kuma bincike kan sauran taliyar.
Abinda Hukumar zatayi kenan cikin satin nan.

Tace, za a bayyana sakamakon binciken wa jama’a in an gama.

Bisa hakan, Hukumar zata fara yin bincike kan Taliyar a kampanonin su yau talata.

A bayanin Hukumar lafiya ta duniya WHO, tace sinadarin ethylene oxide bata da kala, kuma yanada karfi sosai da kashe wutar gas wanda ake amfani da wajen hada wasu sinadaran chemical.

WHO ta bayyana cewa tayi bincike akan dabbobi Kuma ya nuna cewa taliyar tana kara matsalar cancer a jikin dan Adam, kuma a karshe ta nuna ethylene oxide zata iya haifar da cutar, amfani dashi yakamata a rage sosai cikin mutane.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button