Abun Mamaki baya karewa ga Labarin wani matashi a Jihar Yobe wanda ya koma rayuwa cikin ƙogon bishiyar kuka.
Muhammadu wani matashi ne a Jihar Yobe, a wani kauyen karamar hukumar Fika wanda ya hakura da rayuwa cikin garin su ya koma cikin ƙogon bishiyar kuka kimanin shekaru biyar yana rayuwa a cikin ta.
A wani hira da akayi da shi, Muhammadu yace dalilan da yasa na koma cikin ƙogon bishiyar kuka shine nafi jin dadin rayuwa acikinsa fiye da komai.
Ga abinda yace;
Allah yayi masa wata baiwa na sanin abubuwan da zasu iya faruwa cikin kwanaki ko watanni masu zuwa a cikin yawan mafarke-mafarke, Amma idan ya sanar da mutanen garinsu sai suyi masa kallon mahaukaci.
Kullum idan ya basu labarin wani al’amuran da zasu faru sai ƴan kauyen su ɗauke sa mara hankali, hakan sai ta sa yaji bazai iya zama cikin su ba, sai ya koma cikin ƙogon bishiyar kuka wanda yanzu haka yayi tsawon shekaru biyar yana kwana a cikin ta.
Lallai wannan mutumin yanada abin mamaki ga hotunan sa daga bisani.