Yadda Ake Yar Tsame
Yar tsame abinci ne wanda aka fi yi da ci a arewacin kasar. Irinsu Gombe, Bauchi da sauransu. Ga Yadda ake sarrafa Yar tsame cikin kankanin lokaci.
Kayan Hadi
Gero nikakke gwangwani 4
Yeast 1 karamin cokali
Baking powder
Gishiri kadan
Karkashi babban cokali 1
Albasa 1
Flour gwangwani 1
Yadda Ake Hadawa
Ki surfa geronki kiwanke yafita tas kiyanka albasa a akaimiki nika in andawo kizuba yeast,baking powder, gishiri kadan m,karkashi,flour kimotsa karyai ruwa kuma karyai kauri sosai kamar kaurin koko, se kibarshi yatashi kamar 30mins ko 1hr
Ki zuba manki cikin frying pan ki daura a wuta in yayi zafi kifara zubawa da ludayi ko cokali babba in gefe daya yai kijuya dayan gefen din shima inyayi se ki kwashe.
Ana cii da yaji ko kuli kuli