Yadda Ake Tuwon Gero
Tuwon gero tuwo ne wanda aka samo asalinsa a kasar hausa, anfi yin sa da cin sa a arewacin Najeriya. Biyomu dan samun bayani game da yadda ake Hadawa.
Kayan Hadi
Gero
Yadda Ake Hadawa
Idan aka surfe a bushe sai a wanke sai a baza ya bushe sai Akai nika idan a niko sai a tankade sannan a daura ruwa a kan wuta idan ya tafasa sai ayi talge.
Idan talgen ya tafasa sai a rage wuta ya na tasasa kadan kadan sai a debo garin geron a zuba a Kai yayi tozo sai a barshi yayi ta nuna a haka yakai kamar minti arba’in ko hamsin saboda shi Yana da wuyan nuna,kuma ba a rufewa kuma shi gero Yana son wuta.
Sai a tuke shi ya tuku sossai sai a Dan yayyafa ruwan zafi a fai a rufe a bar shi ya turara na tsawon minti talatin aman ba a sa ruwan sanyi haka ma idan za a yi tuwon dawa.
Sai aci da kowace irin miya, daga kan miyan kuka, kubewa, Miyar Taushe da sauransu.
Aci tuwo lafiya