Girke Girke

Yadda Ake Hada Dublan

Dublan abu ne wadda aka fi yi a arewacin Najeriya a lokuta irin na bikin Suna ko aure. Akanyi ne a rabawa mutanen da suka halarci taya murnan biki.

Dublan abu ne mai matukar dadi Kuma mutane dayawa Suna so. Cikin sauki muka kawo muku yadda ake hada dublan domin sarrafawa idan aka ji sha’awa yayin da babu wani biki kusa.

Kayan Hadi

Filawa kofi biyu
Gishiri Rabin Cokali
Sugar Cokali daya
Bakar Hoda (baking powder)
Ruwa kofi uku
Mai Cokali daya
Zuma ko sugar kofi daya
Lemun tsami

Yadda Ake Hadawa

Za’a zuba filawa a cikin dan kwano Sai a Zuba gishiri, sugar da baking powder, sannan a juya.
Sai a zuba ruwa a kwaba tare da zuba mangyada Sai cigaba da juyawa Sai ya kwabu.

Sai a yanka kashi takwas sannan a samu roller ko kwallba Mai tsafta, Sai a mikar dashi Sai yayi fale fale.

Sannan a yanka a tsaye Sai a nade shi irin yadda akeso a so, Sai a soya shi cikin mai me zafi.

Bayan ya soyu Sai a zuba shi cikin matsami.
A daura tukunya a wuta a zuba ruwa kofi daya, in ya tafasa Sai a zuba zuma koh sugar kofi daya
Sannan a matse lemun tsami ciki in ya tafasa Sai a sauka.

Ana iya shafa sugar ko zuma syrup din a jikin Dublan din da brush ko a tsoma Dublan din cikin syrup din a cire Sannan a ci in ya huce.

Ga bayani dalla dalla yanda ake hada Meat PieKunun AyaYar Tsame Da Sauransu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button