
Ita Gwaten doya da wake abinci ne meh matukar inganci wanda ake ci a duk fadin kasar Najeriya. Abinci ne mai Dadi Kuma mai karin lafiya.
A saukake ku biyomu dan koyan Yadda Ake sarrafa wannan abinci.
Kayan Hada Gwaten Doya Da Wake
1. Wake
2. Doya
3. Nama
4. Bushasshen kifi
5. Manja
6. Attaruhu
7. Tattasai
8. Albasa
9. Maggie
10. Citta
11. Tafarnuwa
12. Ganye(Alaiyahu,Ogu ko Ganyen Albasa)
13. Gishiri

Yadda Ake Girka Gwaten Doya Da Wake
- Dafarko zaa wanke wake a daura a wuta ya dafu sosai
- Sai a wanke nama asa su citta da tafarnuwa, albasa, maggi da gishiri a dafa
- Idan yadau dahuwa sai a wanke bushasshen kifin asa su dahu tare bayan ya dahu
- Sai a juye akan dafaffiyar waken a yanka doya en daidai a zuba asa manja da markadadden attaruhu da tattasai da albasa, Maggie da gishiri a rufe.
- Idan yadau nuna sai a zuba ganye ko alaiyahu ko ugu ko ganyen albasa duk wanda de kakeso idan ya nuna a sauke
Gwaten doya da wake ya dahu.