Yadda Ake Hada Cake
Yau Mun kawo muku yadda ake cake, bayan Hadawa zai iya yiwuwa cup cakes ne koh manyan cake ake so depending on dalilin da yasa akayi. Bayan an hada za a iya gasa ta a cikin babban faranti in za ayi bikin birthday, in na Suna ne ko biki Ana iya saka wa cikin kananan faranti dan kowa ya samu shi ake kira cupcakes. Biyo mu a sannu dan ganin yadda ake hada cake a saukake.
Kayan Hadi
Fulawa Kofi hudu
Simas Butter guda biyu
Kwai 14
Vineger Rabin cokali
Sugar Kofi biyu
Baking powder cokali daya
Baking soda Rabin cokali
Flavour duk Wanda kake so
Yadda Ake Hadawa
Zaki zuba suganki akwano tare da butter ki juyashi ya juyo sosai idan kinada electric mixer kiyi amfani dashi, idan bakida shi kiyi amfani da hand mixer idan yayi zakiga ya hade jikinshi yayi fari.
Sai ki fasa kwanki aciki ki juya sosai ya juyu shima sai ya hade sosai.
Sai kisa bakin powder da vanilla extract ko flavour, aciki ki juya, saiki dunga diban flour kina barbadawa kina juyawa a hankali harsai yayi.
Yanayin yadda kwabin cake yake kiyishi kamar kaurin talge wanda yayi kauri, Ba kamar fanke ba anayinshi yadanyi ruwa ruwa kar yakai taurin fanke, saiki shafa butter ajikin kwanon cake din ki xuba kwallin cake din amma rabi sbd idan ya fara gasuwa yana tashi idan kika cika kwanon cake din idan y taso zai zube.
Daganan saiki saka a oven idan cake yayi zakiji yana kamshi, idan kinaso ki tabbatar cikin ya gasu saiki soka toothpick aciki idan kika cire shi babu abinda y makale mai ta cake ya gasu.
Aci dadi lafiya