Yadda Ake Miyar Yakuwa Da Ganyen Albasa
Kayan Hadi
Manja
Nama
Attaruhu
Tattasai
Albasa
Gyada
Maggi
Gishiri
Citta da tafarnuwa
Ganyen Yakuwa
Ganyen Albasa
Yadda Ake Hadawa
Dafarko zaa wanke naman a daura a wuta a daka citta da tafarnuwa asaka,ayanka albasa asa sai asa gishiri da Maggie abar namar ta dafu sannan a juye a kwano
Sai a wanke yakuwan a tafasa shi tafasa daya sai a dauraye yarage tsami
Sa’annan a soya manja a zuba markadadden tattasai,attaruhu da albasa a soya su tare sai a saka dakakkiyar gyada a soyasu asa Maggie da gishiri sai a zuba naman da aka dafa tare da ruwan naman sai asa ruwan sanwan a saka daddawa guda Daya sai a rufe tukunyar
Bayan ya tafaso yafara kaman minti biyar zuwa bakwai sai a saka ganyen yakuwan da ganyen albasa a rufe bayan minti biyar sai a sauke.
Ana cinsa da kowani irin tuwo.