Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Meat Pie

Yadda Ake Meat Pie

Ita meat pie abar marmari ne wadda mafi yawa a kanci wajen biki ko dan marmari. wani lokacin akan karbi baki da meat pie da yar lemo. A yau mun kawo muku yadda ake sarrafa ita kayan fulawa mai suna meat Pie cikin hanya maisauki.

Kayan Hadi

DOWNLOAD ZIP/MP3

Nikakken nama  rabin kilo
Fulawa kilo daya
Albasa daya mai dan girma
Dankalin turawa guda biyar manya
Karas guda 3 manya
Margirine 500g
Maggi 2
Gishiri daidai dandano
Man miya cokalin miya daya
Taim (thyme) rabin cokali
Baking powder cokali biyu tea spoon
Koyi guda daya
Yadda ake hadawa

Filling

Da farko ki bare dankalinki da Karas ki yayyankasu kamar kanana. Ki wanke ki ajiye a gefe
Sai ki dora manki a wuta, idan ya yi zafi sai ki yanka albasa ki zuba.
In albarsan ya soyu (ya dan fara golden brown) sai ki zuba nikakken namarki ki soya har sai ya soyu.

A wannan lokaci sai ki sa thyme na ki da Maggi da ruwa kamar kwatan kofi. A barsu su nuna kamar na minti 30.
Sai ki zuba yankakken dankalinki da yankakken karas naki a ciki a basu kamar minti 20. Sai a dan kwaba Fulawa kadan da ruwa a zuba a ciki don ya yi kauri. A nan sai a sauke a ajiye a gefe. Filling ya kammala.

Kwaba Fulawa (dough).

Ki samu robarki mai fadi ki tankade Fulawarki, kisa baking powder, da gishiri ki hada su sosai.
Sai ki zuba bota, ki hada su sosai su hadu. Sai ki zuba ruwa kadan kadan kina hadawa har sai kin samu hadi mai taushi kamar na cincin.
Abu na gaba shi ne rolling. Ayi rolling din shi fale-fale. Sai a rinka yanka shi kamar girmar murfin kofi round.
Ki fasa Koyi ki kada.

Meat Pie
Meat Pie

Sai a dibi fillings dinnan kamar cokali daya da rabi a zuba a kan yankakken dough din nan, sai a dangwali Koyi kadan a shafa a bakin sai a rufe. A anan za ki iya anfani da cokali mai yatsa a daddatsa bakin don bakin ya rufu da kyau kuma ya bada kamanni mai kyau. Ki rika jera su a oven tray a shafe tray din da bota kafin a jera meat pies din. In kin kare jerawa ki shafe kan pies din da koyi.

Sai ki sa a cikin oven mai zafi preheat oven a barshi har sai ya yi dan brown ko kuma misalin minti 25 za ki ji gida ya baje da kamshi. Shi ke nan meat pie ya kamala.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button