Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Miyan Romo

Yadda ake miyan Romo

Ita Miyar romo miyace wanda ake ci da tuwon sakwara ko na Shinkafa mafi yawan lokuta. Miyan ta kasance cikin miya masu Dadi sosai a kasar hausa da kewaye. Biyomu kadan dan koyar yadda ake hada miyar.

Kayan hadi

Namar rago mai kashi
Attaruhu
Tattasai
Albasa
Tumatur
Chitta
Tafarnuwa
Masoro
Maggie
Gishiri
Mangyada
Ganyan albasa

Yadda Ake Hadawa

Da farkon Za a wanke namar ragon ne sai a daka citta, tafarnuwa, masoro a zuba a Kai da Maggie da gishiri da albasa sai a daura a kan wuta, idan ya fara Kam shi sai a wanke kayan miya ya markada yayyi laushi aman tuna din kadan ne bai fi kamar guda biyar ba,

sai a zuba a ciki a rufe ya cigaba da dafuwa za a bar shi yayi ta dafuwa ne har sai Naman ya bar jikin kashin sai a wanke ganyen albasa a yanka a zuba sai a barshi ya cigaba da nuna sai a sauke.

Kamin nan tuwon mu ya kammala, Sai a zuba a faranti ko kwano dan jindadin miyar romo.

Ana cin shi ne da tuwon sakwara ko semovita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button