Girke GirkeLabaran Yau

Yanda Ake Asillen Zogale (kwadon Zogale)

Yanda Ake Asillen Zogale (kwadon Zogale)

Ita Asillen zogale abinci ne wanda aka fi ci a arewacin Najeriya. Ita Zogale Tana da amfani wajen kara karfin garkuwan jiki na dan Adam.

Kayan Hadi

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ganyen zogale
Tumatur Manya Masu karfi jajaye guda Hudu
Tattasai na 100naira
Albasa Na 50naira
Karago na 100naira
Cucumber (gurji) guda daya
Maggi na 50naira

Asille abinci ne da akan yishi nadan marmari Yana da farin jini idan akayi kasancewan baa fiye yi ba anfi cin shi bayan Karin kumallo haka da hantsi kafin aci abincin rana.

Yanda Zaki Hada

Zaa wanke zogalen a daura asa ruwa Dan daidai a diga kanwa a barshi ya nuna bayan ya nuna sai a juye a matsami ya tsantsame ruwan tas adan matse saboda ruwan yafita dakyau.

Kwadon Zogale
Kwadon Zogale

Sai a juye a kwano asa yankakken tattasai,albasa, cucumber da tumatur da maggi sa’annan asa garin kuliluli a gauraya sai aci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button