Labaran Yau

Ododo Ya Kashe Zaben APC Firamari Na Takarar Gwamna A Jihar Kogi

Ododo ya kashe zaben APC firamari ta takarar gwamna a jihar Kogi

Ahmed Ododo ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar kogi.

Daga bakin sakataren zaben firamarin ta Jam’iyyar APC, Patrick Obahiagha, yace Ododo ya lashe zaben da kuri’u 78,704 wanda ya doke yan takaru 6 ya zama fitaccen dan takara.

Obahiagha wanda bayyana sakamakon zaben yan takarar gwamna ran jumma’a a lokoja, yace Salami Momodu ya sami kuri’u 1,506, Abubakar Yahaya Ashemogu ya samu 1,159, Shaaibu Abubakar Audu ya samu 763.

DOWNLOAD MP3

Ya kara da cewa Stephen Ocheni ya samu 552, Sunusi Oheire yasamu 424 da Kuma Smart Adeyemi ya samu 311 a zaben da akayi.

Sakataren zaben ya bayyana cewa cikin mutane 93,729 masu zabe, 89,419 aka tantance Kuma sukayi zabe.

Ododo ya lashe zaben da akayi ran 14 ga watan Aprailu a shekarar 2023, a jihar kogi an bayyana shi a sakamakon meh yawan kuri’u Kuma yaci zaben APC firamari na takarar gwamna.

DOWNLOAD ZIP

Obahiagha ya yi murnan wa manyan mambobin jam’iyyar wajen gudanar da zaben cikin lumana.

Sakataren kwamitin ya yabawa gwamna dan aiwatar da kudirin demokradiya.

Daily Nigeria suka rawiato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button