Labaran Yau

Hukumar Jami’a Ta Kasa NUC Ta Amince Wa Jami’ar Alhikmah Karin Lasisin…

Hukumar Jami’a ta Kasa NUC ta amince wa Jami’ar Alhikmah kosakosai tara (9)

Hukamar da keh kula da tafiyar da jami’an kasa ta baiwa Jami’ar Al-hikmah na jihar kwara Lasisin karin kosakosai guda tara.

Shugaban Makarantar Farfesa Noah Yusuf, ya tabbatar da hakan wa manema labarai a garin Illorin ran Jumma’a.

Shi Noah ya ce a shekarar 2020 makarantar tasamu amincewar kosakosai 22, wanda Kuma a shekaran 2021 suka samu karin guda 11, a duka in kahada sun samu amincewar kosakosai 42 wanda Jami’ar keh gudanarwa.

A cikin karin bayaninsa, A shekarar da ta gabata 2022 sun kara neman amincewar kosakosai wanda ya hada da English, Agriculture, Human Anatomy, computer science, Education physics, information science, Law, geology da biology.

A fadin shi, sun dau babban mataki wajen samun amincewar kosakosai wanda duka kosakosan sun samu cikakkiyar amincewa.

Duk da hakan akwai kosakosan da basu tsaya a kan kafaffunsu ba tukunna dan neman amincewar hukumar ba. Wanda su ma in sun balaga za a nema musu yancin cin gashin kansu.

Mafi yawan kokasai na matakin digirin farko suna yancin kansu da amincewa na hukumar kasa har na shekaru biyar, wasu zuwa 2025 wasu kuma 2027.

Jami’ar Al-hikmah ta samu lambar zama cikakkiyar jami’an da iyayen da dalibai zasuyi burin kai yara Kuma yara suyi sha’awar shiga don samun amincewar hukumar kasa ta jami’a.

Wannan lambar amincewa da ta samu ya taimaka wajen zama fitacciyar jami’a wanda keh bada ilimi Mai inganci wa Al’umma.

Malam Yusuf yana godewa jiga jigen makarantar wajen jajircewa da taimako wajen cin ma nasaran samun Amincewar.

Yusuf ya kara da cewa jami’an zata yi na farko asusun kyauta na biliyan sha biyar a ranar zagayowar haihuwar wanda ya kirkiro makarantar Ranan Alhamis takwas ga watan yuni.

Shugaban Jami’ar yana rokon gwamnatin jiha da na tarayya dasu bada taimako ta hanun Tetfund wurin samun giran.
Yace jami’u masu zaman kansu na bukatar tallafin gwamnati dan samar da karatu masu inganci wa kasa ya yan kasa.

Ya kara da bada shawara wa gwamnatin jiha da ta turo dalibai wajen karanta law, cyber security, nursing, geology, computer sciences, information systems da kuma Education.

Shugaba buhari ya samu amincewar majalisan tarayya kan kirkiro sabbin wuraren shakatawa na kasa

Majalisan tarayya Ran Alhamis ta Amincewa neman kirkiro sabbin wajen shakawa na kasa guda goma.

Hakan yazo da mabiyi da tallafi Wanda Ado doguwa shugaba a majalisan yayi a Abuja.

Dailynigeria ne ta rawaito
Ni Abdulmatin na gabatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button