Labaran Turanci

ABUN TAUSAYI!! DJ Cuppy Ta Sanar Da Rasuwar Kakarta

Jarumar waka kuma DJ yar Najeriya mai suna Florence Otedola, wanda aka fi sani da DJ Cuppy, ta sanar da rasuwar kakarta ta wajen mahaifiyarta.

Jarumar diya ga hamshakin attajirin wato Femi Otedola ta nuna ta’aziyyarta cikin kunci da imanin cewa kakarta tana “sama” ahalin yanzu.

DJ Cupy Da Kakarta
DJ Cupy Da Kakarta Wanda Ta Rasu

Ta kuma nuna godiyarta kan yadda kakarta ta raine mahaifiyarta cikin kulawa da tarbiya, sa’an nan ita mahaifiyar kuma ta raini ita Cuppy.

Tauraruwar waƙar da ke baƙin ciki ta rubuto a shafinta na X:-

“Mahaifiyar mummy na ta rasu. Kwanciyar hankalina shine sanin cewa tana sama, domin ta nuna mana a iya ƙauna rayuwar da ta yi!

“Na yi matukar godiya da yadda ta siffata mahaifiyata, wacce ta siffata ni. Ina yi wa kaina addu’a a wannan lokacin na canji na kwatsam, amma mun riga mun san cewa Allahnmu nagari ne koyaushe.

“Kaka Kaduna, ruhunki yana rayuwa, yana jagorantarmu kuma yana ƙarfafa mu # RIP.”

Ga Asalin Post Dinda Tayi A X Daga Bisani ⇓

Yi mata ta’aziya a comment section 👇

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button