Mulkin Mallaka Da Karbo Yancin Kasar Najeriya
Duk da cewa turawan mulkin mallaka ne suka kafa ilimin boko a Najeriya, ba wai don samar da ci gaba ba ne, sai dai an bullo da shi ne a matsayin mafita ga matsalolin yaruka da aka samu a wancan lokacin da kuma bukatar wayar da kai, ta hanyar samar da wasu ’yan kasar da za su karbi mukaman da Turawan mulkin mallaka suka karbe lokacin zuwan su kasar na farko.
Mulkin mallaka wata bukata ce ta tattalin arziki, zamantakewa, da addini wanda aka yi amfani da shi don murkushewa da, sauya tsarin zamantakewar Afirka da kuma tsarin zamantakewar Najeriya.
Hakan ya samu ne ta hanyar musanya tsoffin ka’idoji, dabi’u da ayyuka da hanyoyin ‘yan mulkin mallaka, tanade-tanaden kundin tsarin mulkin da aka tilasta wa ‘yan Nijeriya da nuna wariya, kuma abin da wannan tanadin tsarin mulkin ya samu shi ne raba Nijeriya da bukatunta na ci gaba.
Mulkin mallaka ya yi amfani da ’yan kwadagon Najeriya ta yadda kamfanonin Turawa suka ci riba fiye da ’yan Najeriya da kansu. Haka kuma ya takaita shigar da ‘yan Najeriya shiga harkokin siyasa a cikin batutuwan da suka shafi tafiyar da mulkin kasar.
Wadannan kurakuran da ake ganin na mulkin mallaka ne suka haifar da kishin kasa a Najeriya wanda aka fi sani da `kungiyoyin adawa`. ’Yan Najeriya kamar sauran al’ummomin duniya da aka yi wa mulkin mallaka, sun nemi ‘yancin kansu.
Duk da haka, sabanin al’ummomi kamar Amurka a yakin ‘yancin kai na Amurka (1775), Algeria a yakin Aljeriya (1955), da Haiti a juyin juya halin Haiti (1791), Najeriya ta sami ‘yancin kai ta hanyar ƙungiyoyi masu zaman kansu cikin ruwan sanyi kuma ba tare da yaki ko
cin zarafi ba.
Asalin yan kasar da suka hada kansu guri guda, wanda ya hadar da `yan kabilar Igbo wadanda sune suke mazauna kudu maso gabacin kasar, kabilar yarbawa wadanda sune mazauna kudu maso yammacin kasar da kuma uwa uba hausawa wadanda sune mazauna arewacin kasar wanda sune mafi girma kuma wanda ke da mafi yawan alumma har a wannan lokacin.
Bayan dibar shekaru masu yawa ana mulkin kasar ta Najeriya a wannan tsari na mulkin mallaka wanda turawa sukayi, an samu jajirtattun yan kasa irin su Abubakar Tafawa Balewa, Ahmadu Bello, Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da sauransu da suka tabbatar da cewa kasar Najeriya ta dawo hannun wadanda suke asalin yan kasa, domin ci gaban kasar ya tabbata.
Daga cikin wanda suka sha gwagwarmayar sun hada da:
Daga kan Tafawa Balewa wanda shine Shugaba (Prime Minister) na farko bayan Kasar Najeriya ta dawo hannun `yan Kasa, Da kuma zababben Shugaban Najeriya na farko wato Nnamdi Azikwe da sauransu, sun sha namijin aiki wajen samar wa Kasar `yancin nata a shekarar 1960.
Ga takaitaccen bayani akan wasunsu
AHMADU BELLO
Ahmadu Bello shine gwamnan arewacin Najeriya na farko kuma na karshe, ya rike mukamin (Nothern Premiere) daga shekarar 1954 zuwa 1966.
Ya kuma jagoranci jam’iyyar mutanen arewa NPC, Ya taimaka wa zaben neman yanci a Majalisa, inda ya jagoranci nasarar zaben a shekarar 1959.
A matsayin sa na Sardaunan Sokoto, masauratar da ta ke tushen sa, sanadin da ya sanya shi ya zama daga cikin masu karfi da fada aji a kasar.
Tarihi ya bayyana cewa zaben da akayi wanda ya kai ga samun yancin Najeriya a 1960, ya samo tushe ne wajen hadakar Jam’iyyar NPC da ke karkashin Ahmadu Bello da kuma jam’iyyar NCNC karkashin Jagorancin Nnamdi Azikwe wanda ya kawo Najeriya da muke mora har a yau.
Bello ya zabi ya shugabanci Arewa dan ya zauna kusa da mutanen sa `yan Arewa. Ya rasu yayin da akayi juyin mulki na soji a watan Junairu 1966. Soja Chukwuma Nzeogu ne ya kashe Sardauna.
Daga cikin ababen da ake tuna sardauna da su sun hadar da Jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zaria wadda aka sanya mata sunansa da kuma rawar da ya taka wajen kafa ta da sauran ci gaban da ya samar a arewacin kasar.
A yau hoton Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto shine a kan kudin Najeriya Naira Dari biyu (200).
NNAMDI AZIKIWE
Azikwe ya kasance daya daga cikin jagororin da suka yi fafutuka wajen samun yancin kasa Najeriya. Ya dau tsahon lokacin yana fafutukar aiki dan kawo karshen mulkin mallaka na turawan burtaniya.
Ya fara ne da aikin jarida daga bisani ya zamo dan siyasa. Azikiwe shine shugaban kasa (Governor General) na Najeriya bayan cin zabe da yayi na Gwamnatin farko a shekarar 1963, Kuma ya zama na karshe a shekarar 1966.
Ya shiga harkar siyasa a shekarar 1944 sannan suka hadu suka bude jam’iyyar NCNC wato (National Council of Nigeria and Cameroun) bayan bunkasar da yayi a aikin jarida.
Shi ya kawo kungiyar `Zikist` wanda suke tafiyar neman yancin kasa da Afirka gaba daya dan samun yancin mutanen nahiyar wajen gudanar da mulki da bunkasa tattalin arziki.
Tun shekarar 1940 Azikiwe ya dauke tsahon lokaci yana neman a kawo karshen mulkin mallaka na turawan burtaniya, a 1943 ya hada kai da manyan yan jaridun Afrika ta yamma wajen bayyana kudirin samun yancin.
Ya Kuma nemi rage yawan turawa wajen gudanar da siyasa a inda aka sako yan Najeriya a wasu mukaman yankunan su har ya kai ga neman yancin gaba daya na yammacin Afirka na mulkin turawan burtaniya.
Azikiwe ya mutu a shekarar 1996 ya bar gurbin shi a tarihin Najeriya, wanda labarin sa ya nuna labarin jarumta, da kishin kasa, wanda ya bar ababen yabo da `yan kasa zasu bashi.
ABUBAKAR TAFAWA BALEWA
Bayan Jam’iyyar NPC ta ci zaben samun yanci, Tafawa shine maitamakin jagoran jam’iyyar, daga nan yazama Prime ministan Najeriya, mukamin da ya riqe har watan Junairu na shekarar 1966, inda aka kashe shi a juyin mulkin Soji.
Lokacin sa, Tafawa balewa yana daga cikin masu kawo dokokin da suka taimaka wajen samun cigaban kasa, sanadiyar da ya samu sanuwa a kasheshen waje daga shekarar 1960 zuwa 1961. Daga nan ya samu karin mukami na riqe ministan kasa da kasa.
Abubakar yana daga cikin shugabannin da suka kirkiro kungiyar hadin kan Afirka. Tun daga shekarar 1950, ya kasance yana aiki tukuru dan samun yancin kasa wanda ya takarawa wajen canza dokar kasa har ya kai da samun yancin 1960.
Dattijon arziki ne Mai kishin kasa wanda halayen sa da karamcin sa da ilimin sa ba boyayyu bane. Sir. Abubakar Tafawa Balewa Saurauniyar ingila ta ke kiranshi.
An binne shi a garin Bauchi, Ana kiran wurin Sir Abubakar Tafawa Balewa Tomb dake cikin ganuwar Bauchi.
OBAFEMI AWOLOWO
Obafemi Awolowo shine mutum na farko da ya fara shugancin kudu maso yammacin Najeriya a matsayin (Premiere of Western Region) daga shekarar 1954 zuwa 1960. Yana daga cikin wanda suka jajirce wajen samun yancin kasa.
Wasu Suna ganin shi a matsayin wanda ya nemo tsarin shugabancin na federal system. Wanda zai kawo raba daidai na arzikin kasa. Ya jagoranci Jam’iyyar Action Group AG, yana gaba gaba wajen kawo tsarin federalism wanda hakan ya kai da kawo sabuwar dokar kasa lyttleton ta shekarar 1954.
A matsayin sa na shugaban adawa na Gwamnatin, ya jima yana kalubalantar dokokin tafawa balewa na jam’iyyar NPC wanda yake mulkin kasar. Mutane da dama na yiwa Awolowo ganin yana aiki da turawan burtaniya.
Awolowo ya kasance mai son demokradiyya wanda yayi kokari wajen nuna hakan. Kuma ya taimaka wajen mulkin kai na Najeriya dan samun cigaba na tattalin arziki da muhalli musamman a kudu maso yammacin kasar.
HERBERT MACAULAY
Yana da lakani Baban Najeriya, Herbert Macaulay yana daga jikin manyan jiga jigan da suka taimaka wajen fara neman yancin kasa.
A shekarar 1920 lokacin da kasar Najeriya ta fara fuskantar korafi na siyasa yayinda aka fara tafiyoyin neman yanci, Macaulay yana daga cikin wanda suka fara korafi kan dokokin Yan mulkin mallaka.
Wanda ya shafi ruwa, matsalar filaye, da gudanar da jirgin kasa.
A wannan lokacin, a shekarar 1923, ya kirkiro jam’iyyar NNDP (Nigerian National Democratic Party). Ita ce jam’iyyar ta farko da ta fara lashe kujerun Majalisar kasa.
Zuwa 1930 jam’iyyar ta hada kai da kungiyar matasa wanda suka hadu suka kirkiro jam’iyyar NCNC. jam’iyyar NCNC ta samo asali ne dan neman yancin Najeriya.
ANTHONY ENAHORO
An samu rahoton cewa Enahoro shi ne dan siyasa da ya fara kawo maganar yancin Najeriya a Majalisa a shekarar 1953, Duk da dai ba a samu nasara ba.
Samun yancin ya samu matsala lokacin saboda rashin goyon baya na yan Arewa wanda sunki saboda nasu dalilan.
Duk da bai samu nasara a Majalisar ba, amma hakan da yayi ya taimaka wajen fito da sabuwar kungiya cikin Majalisan wanda suka dage dan yan mulki mallaka su bawa yan kasa karagar mulki.
Daga baya ne aka samu korafi na su Abubakar Tafawa balewa da Remilekun Fani-Kayode tsohon mataimakin Premier na Kudu maso yamma. Wanda hakan ya kai da samun yanci a shekarar 1960.
A matsayin sa na ciyaman na jam’iyyar NADECO (National Democratic Coalition), ya kalubalenci mulkin Sani Abacha kamin Abacha Ya mutu a shekarar 1998.
FUMILAYO RANSOME KUTI
Fumilayo ta kasance Tana adawa da masu mulkin mallaka a Najeriya. Wadda ta taka rawar gani wurin nemo yancin Najeriyar. Tayi amfani da yan kasuwa mata wajen yin zanga zanga kan mulkin Mallaka.
Ta dauke tsahon lokacin tana korafi akan dokokin yan mulkin mallaka wanda ya shafi haraji da hukuma hanyar zantar da hukunci kan lamuran mutanen kasa baki daya.
Abu da ke cikin rayuwar ta da ba a mantawa dashi shine lokacin da sojoji sama da dari suka shiga gidan dan ta Fela Kuti a shekarar 1977, ranan 18 ga watan fabrailu. Wanda ke da Alaqa da mutuwar ta.
Tana da shekara 76 lokacin da aka jefota daga gidan sama, Mai hawa biyu Kuma ta samu rauni hakan ya kai ga mutuwar ta ran 13 ga watan Afrilun shekarar 1978.
Wadannan kadan daga cikin wadanda suka bada gudummawa wajen karbo `y`ancin Najeriya daga hannun zalunci da tsangwama da nuna banbanci da aka sha tsahon shekaru masu yawa a hannun Turawan Buetaniya kuma daga bisani duk wani ci gaba da kasar nan ta samu ya samu ne sanadiyyar gudummawar wadannan `yan Najeriya da abinda sukayi ba abun a manta da su bane.
Daga: Abdulmatin Salihu Dumswak Da Abdullahi Sudawa