Banida Dan Takaran Ko Wace Kujera- Gomna Bala Kaura
BA NI DA ƊAN TAKARA A KOWACE KUJERA – INJI GWAMNA BALA YAYIN TARON MASU RUWA DA TSAKI NA PDPn JIHAR BAUCHI
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yace gwamnatin sa za ta cigaba da tafiya da kowanne ɗan jam’iyya, shugabanni, dattawa, mata da matasa inda ya ƙara da cewa shi na kowa ne ba shi da ɗan takara a kowace kujera.
Gwamna Bala na jawabi ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a matakin jiha inda ya ta’allaƙa nasarorin da gwamnatin sa ta cimma da goyon bayan da al’umar jihar Bauchi ke ba ta.
A cewar Gwamna Bala, dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun tallafa wajen samun nasarar sa wanda a saboda haka jihar Bauchi ta samu sauyi fiye da baya.
Taron, a cewar Gwamna Bala, zai tattauna batutuwan da suka shafi sabbin dokokin zaɓe da kuma hanyoyin kai ga nasarar karɓar ragamar shugabanci a Najeriya ta hanyar haɗa kai.
Gwamna Bala sai ya yabawa tsarin shugabancin jam’iyyar PDP matakin jiha tare da kira ga membobin jam’iyyar da su cigaba da marawa gwamnatin sa baya don cigaba da shan romon dimokraɗiyya da nagartaccen shugabanci.
Taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Alhaji Hamza Ƙoshe Akuyam, mataimakin gwamna Sanata Baba Tela, Sanatoci Abdul Ningi, Adamu Gumba, Bala Kariya, ƴan majalisu, kwamishinoni da sauran su.
Lawal Muazu Bauchi
Mataimakin gwamna na musamman kan kafafen ƴada labarai na zamani
21 Maris, 2022.