Labaran Yau

Matar Shahararren Dan Wasa Ta Nemi Ya Sawwake Mata Kuma Kotu Ta Bata Rabin Dukiyarshi

Matar shahararren dan wasa Achraf Hakimi ɗan asalin ƙasar Marocco ta nemi da ya sawwaƙe mata sannan kuma kotu ta sa ya bata rabin duk dukiyar da ya mallaka.

Sai aka sanar da ita cewa ai shi Hakimi ɗin bai mallaka komai ba, domin duk dukiyarsa ya sanya sunan mahaifiyarsa ne akai.

Ana biyan Achraf zunzurutun kuɗi dai har Miliyan €1 daga ƙungiyarsa ta PSG a duk wata.

Amma kaso 80% duk sai ya rubuta a riƙa turawa asusu mai ɗauke da sunan mahaifiyarsa Hajiya Fatima.

Don haka shi kawai ƴan canji yake da shi kaso 20% wanda yake gudanar da rayuwarsa da matarsa.

Duk manyan kadarori kamar gidaje, motoci, gwala-gwalai da sauran kayan alatu har ma suturu masu tsada suna ɗauke ne da sunan mahaifiyarsa.

Kuma duk sanda yake buƙatar wani abu sai ya tambaye ta ta saya masa.

Ya kamata ayi koyi da wanga hali na Hakimi, saboda Anzo aci banza, Amma banza bata samu ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button