Labaran Yau

Monoma Sunyi Watsi Da Kasancewar CBN Cikin Sabon Tsarin Na Samar Wa Kasa Abinci

Monoma Sunyi Watsi Da Kasancewar CBN Cikin Sabon Tsarin Na Samar Wa Kasa Abinci

Domin Najeriya ta samu wadatar abinci, da inganta hanyoyin samar da kimar noma da samar da ayyukan yi ga dimbin matasanta, dole ne ta fara magance matsalolin da ke akwai, tare da kawar da cin hanci da rashawa a cikin shirye-shiryenta na shiga Tsakani. A cewar manoman.

Manoman, wadanda suka mayar da martani ga sanarwar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na samar da wadataccen abinci da kuma ayyana dokar ta-baci, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta cire babban bankin Najeriya (CBN) daga kula da duk wani asusu na kudaden da akayi niyyar warewa Shirin.

Shugaba Tinubu dai yana shirin tura ajiyar kudi daga tallafin man fetur zuwa bangaren noma don inganta fannin da kuma bunkasa gudunmawar maganar noman abinci, ta yadda zai ishi kasar gaba daya.

Amma manoman sun ce idan ana son faruwar hakan toh, dole ne shirye-shiryen gwamnatin su kasance na gaske, aiwatar da su yadda ya kamata da kuma samar da su a cikin bankin noma don tabbatar da manoma na gaske sun ci gajiyar shirin.

“Dole ne a cire ikon da CBN ke da shi idan da gaske wannan gwamnatin na son yin nasara. Dole ne kuma tayi tsayin daka wurin kawar da cin hanci da rashawa a cikin shirye-shiryenta, ”in ji Jude Obi, shugaban kungiyar masu aikin noma ta Najeriya, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan kudurorin nasu.

“Dole ne gwamnati ta magance wadannan matsalolin. Idan ba`ayi hakan ba kuwa, Shirin zai zama kamar sauran shirye shirye da akayi a baya wadanda kuma basu cimma gaci ba” in ji Obi.
An soki babban bankin saboda rashin kula da shirin Anchor Borrowers – babban shirin gwamnatin da ta gabata na samun wadatar abinci.

Monoma Sunyi Watsi Da Kasancewar CBN Cikin Sabon Tsarin Na Samar Wa Kasa Abinci
Monoma Sunyi Watsi Da Kasancewar CBN Cikin Sabon Tsarin Na Samar Wa Kasa Abinci

Rashin biyan miliyoyin manoman kudaden ya nuna raunin da shirin shiga daukin gwamnatin ya samu tare da karancin amfanin da kasar ke samu a shekara, idan aka kwatanta da takwarorinta na Afirka.

“Ina fata da gaske cewa shirin shugaban kasa zai cimma nasarar samar da abincin,” in ji Ibrahim Kabiru, shugaban kungiyar manoman Najeriya.

Kabiru ya bukaci gwamnati da ta sake tantance shirye-shiryen da ake kokarin aiwatar wa, kuma a watsar da CBN daga bangaren domin tabbatar da gaskiya da aiwatar da aikin yadda ya kamata.

Kamata yayi Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da hadin gwiwar kungiyoyin manoma daban-daban su samar da shirye-shiryen shiga tsakani, ba tare da babban bankin ba, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button