Labaran Yau

Niger Delta Zasu Bawa Tinubu Goyon Baya cewar Asari Dokubo

Shugaban kasa Bola Tinubu ya samu goyon baya wajen mutanen Neja delta wajen yaki da satar mai dan yelwantuwar tattalin arzikin kasa.

Asari Dokubo, ya bayyana goyon bayan yayin da ya ziyarce shugaban kasa a Abuja ranar jumma’a.

Dokubo yace Albarkan arzikin kasan na yankin na hanun daidaikun mutane yan Najeriya wanda suke amfanuwa dashi fiye da sauran mutanen kasar.

DOWNLOAD MP3

Ya ce masu neman yancin yankin Neja delta zasuyi kokarin samo yanci na arzikin kasa dan amfanuwan talakan Najeriya.

“Mun san satar mai Tana hannun masu karfi ne daga cikin yan Najeriya, wanda ya hada da sojoji wanda suke bada umarni daga Abuja, Mun jima Muna fadan hakan amma mutane dayawa basu fahimci siyasar satar mai ba.

“Na fadawa shugaban kasa cewa mun san wanda suke da hannu ciki, Kuma laifin satar na faruwa ne kusa da wanda ke tsaron satar nan.

DOWNLOAD ZIP

“Jami’an tsaron Suna batawa wanda suke diban mai ta hanya mai kyau lokaci, yakamata muyi magana dan kawo karshen wannan matsalar dan kawo yelwantuwar tattalin arzikin kasa.” Cewar sa.

Mista Dokubo yace sunyi zama na tattaunawa da shugaban kasa, kuma Duk wanda suke jawo koma baya za a dakile su a yankin Neja delta.

Ya kara da cewa kasar bai kamata ya zama yana hannun daidaikun mutane ba. Wanda basu damu da cigaban Neja delta da Najeriya gaba daya ba.

“Zanyi aiki da jiga jige dan kawar da satar mai, mu kawo karshen hakan da Kuma yaki da Duk wanda zai kawo cikas na tattalin arzikin kasa.” Dokubo yayi Alwashi.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button