AddiniLabaran Yau

Hukuncin Bayyana Karatun Sallah Ga Mata 

Hukuncin Bayyana Karatun Sallah Ga Mata 

Annabi SAW yace kuyi sallah kamar yadda nakeyi, ko a zamanin Annabi ko sahabbai bamu ga banbancin yin Sallah ba. Sallar magrib raka’an farko guda biyu zaki bayyana, sallar isha’i zaki bayyana raka’a biyu na farko Ki boye biyu na karshe haka zaki bayyana sallar Asuba.

Wannan shine qa’ida na sallah.

Ummul Darda ta kasance tanayin sallah kamar yadda maza suke sallah kuma malama ne masanan fiqihu, Saboda haka mace zatayi sallah inda maza suke sallah. Inda aka bayyana itama ta bayyana, inda aka asurta. Sai dai kawai a inda shariah ta  shardanta shine zata sirranta, a ina ne shari’a ta saba? Idan zatayi sallah a cikin jama’a wa inda ba muharramanta ba, indai zatayi karatu kuma anaso a daadada karatun, wannan zai iya sa maza su fitinu da jin dadin karatun ta, to a nan wajen sai ta asurta.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Haka fuqaha’u suka ce zata asurta ko da na bayyana wa ne, Amma in adakin ta ne zatayi sallah ko kuma a inda mijinta da yayanta da yan uwanta mata ko yan uwanta maza muharraman ta ko sallar magrib ko isha tayi a bayyane. Don ta samu lada nayin sunnah, shine asalin qa’ida. Kamar yadda Abuhuraira yake cewa munyi sallah a bayan Annabi SAW abinda yajiyar damu muna bayyana muku , abinda ya asurta a garemu muna asurta muku. Malamai sun nuna hakan shine sunnah.

Adduar Da Akeyi Bayan Tada Iqama

Bayan Kabbara kamin ka fara karatun sallah “Allahumma, inni a’udhu bika min fitnatin-nari, wa ‘adhabin-nari, wa fitnatil-qabri, wa ‘adhabil-qabr, wa sharri fitnatil masihid-dajjal, wa sharri fitnatil-faqri, wa sharri fitnatil-ghina. Allahummaghsil khatayaya bima’ith-thalji wal-baradi wa anqi qalbi minal-khataya kama anqaitath-thawbal-abyada min ad-danasi, wa ba’id baini wa baina khatayaya kama ba’adta bainal-mashriqi wal-maghrib. Allahumma inni a’udhu bika min al-kasali wal harami, wal ma’thami wal-maghram”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button