Biography

Cikakken Tarihin Ali Nuhu, Rayuwarsa, Karatunsa, Sana’arsa, Kannywood, Karramawarsa, Iyalansa, Arzikinsa, Siyasarsa, Hotinansa

Cikakken Tarihin Ali Nuhu

Yau shafin labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihi da bayani kan Jarumi Ali Nuhu.

Rayuwar Ali Nuhu

Ali Nuhu Muhammed wanda aka fi sani da Ali Nuhu ya kasance dan wasan kwaikwayo ne wanda ya shahara kuma yayi fice a haryan shirya fina finai, bada umarni, rubuta labari, da kuma rawa.

An haife shi ran 15 ga watan Maris ta shekarar Alif dubu da dari tara da saba’in da hudu 1974 a maiduguri. Mahaifansa sun hada da Nuhu Paloma da Fatima karderam. Ali Nuhu ya girma zuwa zama daya daga cikin manyan yan fina finai a arewacin Najeriya wanda ake so kuma ake yabo a cikin masana’antar fina finai a kasar.

DOWNLOAD MP3

Tashin sa, Ali Nuhu ya nuna soyayyar sa wa harkan fina finai, wanda ya koya yayin karatu da yake yi na boko.

Karatun Ali Nuhu

Ali Nuhu ya samu ilimin firamare a Riga special elementary school inda ya kammala matakin farko na boko a jihar kano, nan ya wuce gaba inda yayi karatun sakandare a science secondary school Dawakin.

DOWNLOAD ZIP

Soyayyar sa ga boko ta kai shi karatun jami’a a jami’ar Jos inda ya kammala digirinsa ta farko ya kuma karanta Geography.

Ya kuma tafi yayi diploma kan shirya fina finai da cinematic arts a jami’ar Southern California.

Domin samun kwarewa a harkan fina finai, ya kuma yi wata diploma a new delhi na kasar India.

Shigar Ali Nuhu Kanywood

Shigar Ali Nuhu kannywood ya samu asali ne lokacin da yake koyan acting a jami’ar Jos. Inda yaje inda ake audition na yan fina finai wanda ya canza masa rayuwa.

Hakan ya kawo gwargwarmaya da yayi cikin masana’antar a shekaru Ashirin da suka gabata.

Basirar sa da iyawar sa ta nuna kai lokacin da yayi bautar kasa a jihar oyo garin Ibadan. Inda ya shiga fannin waka da drama.

Ya wakilci jihar Oyo a gasar drama na NYSC inda ya nuna kwarewar sa wa kasa.

Bayan kammala bautar kasa yayi film dinsa  mai suna “abin sirri ne”.  Ya samu shiga wannan fim din bayan ya nuna iyawarsa a fim din Sangaya wanda ta nuna shi wa idon duniya.

Bawai fim din sangaya ne ta kawo mishi nasara ba, Amma sangaya ta kasance fim da tafi shahara a wannan lokacin. Hakan ya bayyana Ali Nuhu ta fuska mai kyawu masana’antar.

Ali Nuhu ya kasance ana ganin shi cikin fina finai daban daban a kannywood. Kwazon shi da basirar shi a manya manyan fina finai kamar su Azal, Dijangala, Wasila, da mujadala cikin fina finai. Kwarewar sa ta nuna ko a cikin masu korafi basu iya karyata hakan ba.

A shekarar 2019, Ali Nuhu yayi murnan cika shekara Ashirin a harkan. Yanada fim sama da 500.

Karramawar Ali Nuhu

Ali Nuhu ya bada Gudumawa a masana’antar fina finai kuma babu wanda zaice bai Sani ba. Hakan ya sa ya samu Karramawa daban daban, fara da Karramawar AMAA Africa Movie Academy Awards.

Karramawar Best of Nollywood Awards (BON), Karramawar City People Entertainment Awards, Karramawar Nigerian Entertainment Awards (NEA), da sauransu.

Karramawar tazo ne bisa jajircewa da kuma aiki tukuru dan kawo cigaban masana’antar fim.

Iyalen Ali Nuhu 
Iyalen Ali Nuhu

Iyalen Ali Nuhu

Ali Nuhu Yana da aure, ya auri Maimuna Garba Ja Abdulkadir, Yana yara uku wanda sun hada da Fatima babbar yarsa sannan kuma kaninta mai binta wato Ahmad wanda ya kasance Yana fim kuma a Yanzu Yana makarantar kwallo.

Duk Yadda aikin sa yake na fim Amma yayi kokari wajen samun lokacin aiki daban da kuma lokacin iyalensa.

Arzikin Ali Nuhu

Ali Nuhu ya kasance mai fada aji a masana’antar kannywood, Yana da arziki kimanin dala miliyan biyar. Ya samu kudade da arziki a masana’antar kannywood da kuma wasu kasuwanci da yakeyi a gefe.

Cigaban Ali Nuhu yazo ne bayan jajircewa, kwazo da basirar aiki da hada.

Kuma ya kasance mai yawan taimako a fanni daban daban kamar daga sabbin yan wasanni, tallafawa gidan marayu da sauransu.

Siyasar Ali Nuhu

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Ali Nuhu da ya zama darakta Janar na hukumar fina finai na Najeriya.

Hotunan Ali Nuhu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button