Labaran Yau

Sabon Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umurni A Binciki Tsohuwar Gwamnatin….

Sabon Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umurni A Binciki Tsohuwar Gwamnatin Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu Sokoto ya kafa kwamitin bincike da zai binciki duk wani rabon fili da kadarorin gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjonsa a zamanin Gwamna Aminu Tambuwal.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai Magana da yawum gwamnan a safiyar jiya asabar.

Gwamnan ya kafa kwamiti mai mutum 5 ya kasance karkashin jagorancin mai shari’a M.A. Pindiga (rtd) yayin da Barista Nasiru Muhammed Binji zai zama Sakataren ta.

DOWNLOAD MP3

Sauran manbobin kwamitin sun hada da Chief Jacob E. Ochidi, SAN; Alhaji Usman Abubakar da kuma Barrister Lema Sambo Wali.

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai yi nazari kan yadda aka raba filaye daban-daban a duk fadin Jihar ciki har da gidajen gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjo da su.

 

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button