Labaran Yau

Gwamna Yusuf Ya Biya Naira biliyan 1.5 Na Jarabawan NECO A….

Gwamna Yusuf Ya Biya Naira biliyan 1.5 Na Jarabawan NECO A Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta Kashe kudade naira biliyan daya da rabi wajen biyan kudin Jarabawan NECO wa dalibai dubu hamsin da bakwai na Makarantun gwamnati a jihar baki daya.

Hakan ya fito daga bayanin Ibrahim Shuaibu, Sakataren Zantarwa na ofishin mataimakin gwamnan Kano Aminu Gwarzo.

Yace Gwamna Abba Yusuf Kabir ya bayyana hakan lokacin da za a bude fara Jarabawan a kwalajin Rumfa a garin Kano.

Inda Gwarzo ya wakilce shi, Yusuf ya jaddada cewa biyan kudin jarabawan yana daga cikin dokar gwamnati wajen canza fuskar ilimi ta inda zai bunkasa inganci da biyan bukata na cigaba.

Ya bada karfin gwiwa wa dalibai wajen jajircewa dan tabuka wani abu domin cin Jarabawan dan cimma burin tallafi da gwamnati ta yi dan bukasa ilimi.

“Yakamata ku zage damtse da Kuma nutsuwa dan ku samu sakamako Mai kyau bayan Jarabawa, wanda zai faranta wa jiha da iyalinku rai” Cewar sa.

A Jawabin kwamishinan ilimi, Umar Doguwa, ya bayyana cewa akwai kwamiti wanda jihar ta kirkira wajen duba da lamarin kulle Makarantar kwana da akayi domin a bude ta.

Ya yabawa gwamnatin jiha wajen cigaba da ciyar da dalibai da akeyi a Makarantun gwamnati, yace ababen zama za a karo a Makarantun babu jimawa.

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button