Bayan Idona Ya Fita Da Aka Harbeni Na Mayardashi Da Hannunna – Zazzaky
Shugaban Kungiyar Shia Ta Nigeria Ibrahim El Zazzaky Yace lokacin da sojojin Nigeria suka budr mishi wuta, harbi ya sameshi a ido wanda har yayi sanadiyyar fitowan idonshi na barin hagu, nan take a bayaninshi ya mayar da idanun da hannunshi.
Zazzaky yayi wannan bayanine a wata video dayake jawabin, kadan daga cikin abubuwan da suka faru dashi lokacin fafatawarsu da sojojin Nigeria.
Wannan jawabi ya jawo cece kuce dayawa a kafafen sada zumunta na zamani, ko ya Jama’a suke ganin wannan abun al’ajabi na Malam Ibrahim Zazzaky?