Labaran Yau

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Damke Asari Dokubo A Halin Yanzu

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Damke Asari Dokubo A Halin Yanzu

Akwai kiraye kiraye da matsi da gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Asiwaju Tinubu akan sai ta damke tsohon jagoran `yan tada kayar baya na Niger Delta Asari Dokubo.

Cikin watan da ya gabata ne dai aka ga faifai na video wanda ke nuna Dokubo din riqe da bindiga kirar AK-47 YANA Iqirarin hallaka yan kabilar Igbo baki dayan su.

Cikin video din ya nuna baya tare da su, kuma ya kara da cewa yayi niyyar ya sayar da su kamar bayi amma sai Ingila ce ta cece su.

DOWNLOAD MP3

Gwamnatin tana shan matsi ne daga yan kungiyoyi daban daban wanda ke nuni da cewa kada ta yadda ta bar Dokubo din haka nan, abinda ya kamata ayi shi ne a kame shi a kulle saboda wannan bidiyo da ya saki.

Jagoran kungiyar HURIWA wanda shi ya bada sakon ga gwamnatin yayi bayani a turance da cewa `Tilas ne hukumar farin kaya ko wata hukumar ta tsaro ta kama Dokubo Asari domin zargin sa da sukeyi da hannu tsamo tsamo kan abubuwan da ke faruwa a bangaren inyamurai wato Kudu Maso Gabacin Najeria.

Kuma jagoran ya ceh lokaci yayi da duka yan kabilar igbo din zasu fara zanga zanga a dukkanin bangaren kasar nan domin tabbatar da gwamnatin ta cika masu burin na su na kame Dokubo.

DOWNLOAD ZIP

Kungiyar HURIWA ta bawa shugaban kasa Tinubu awanni 72 don aiwatar da wannan bukata ta su a fadin jagoran HURIWA din kuma zasu kira sauran `yan uwansu da suyi zanga zanga a birnin tarayya a sati mai zuwa.

HURIWA me ikrarin cewa wannan rashin tarbiyya da nuna tsana ga dukkanin yan kabilar Igbo din da Dokubo yayi bai kamata ya wuce hakanan ba tare da an hukunta wanda ya aikata abin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button