Labaran Yau

Onana Na Shirin Canja Sheka Zuwa Manchester United

Onana na shirin canja sheka zuwa Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake ingila tana shirin daukar Andre Onana. Mai tsaron ragar dan shekara 21 dan asalin kasar kamaru yana cikin zaratar yan kwallon kafa a nahiyar turai da suka nuna kwarewa sosai a gasar kwararrun ta nahiyar turai a shekarar data gabata.

Biyon bayan karewar kwantaragin mai tsaron ragar Manchester United dan kasar andalus David de gea Wanda Manchester United basu sabunta masa shekarun aikin ba, masana a harkar kwallon kafa anan gida da kashashen waje na ganin cewa Onana shine zai maye gurbin De gea.

Onana dai a shirye yake domin kara aiki da mai horaswa Erik ten haag Wanda sukayi aiki a kungiyar Ajax dake babban birnin Amsterdam a kasar Holland.

DOWNLOAD MP3

Rahotannin da muka samu sun nuna cewa jiya a ibiza wakilan Dan wasa onana da na Kungiyar Manchester United sun gana domin shirya ciniki cikin kankanin lokaci duba da yadda mai horaswa Erik ten haag ke fatan ya kammala daukan yan wasannin dake cikin tsarinsa kafin tafiya wasannin atisaye a kasar amerika cikin wannan watan.

Akwai rade radin cewa kungiyar dake kasar ingila na shirin mika tayin dala miliyan hamsin.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button