Labaran Yau

Bajin Farko Na Tallafin Karatu Zuwa Kasar Waje Na Kano Zasu Tafi A Satumba

Bajin Farko Na Tallafin Karatu Zuwa Kasar Waje Na Kano Zasu Tafi A Satumba

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yace bajin farko na scholarship wato tallafin karatu wa yan Kano zasu fara karatu a jami’o’in su a watan Satumba.

Rahoton yazo daga bakin Mai Rikon kwaryar Press Sakatare, Hashim Habib a Kano ran Asabar.

Yusuf ya bayyana hakan a gidan gwamnati lokacin haduwan shi da Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da mambobin masarautan lokacin sallah.

DOWNLOAD MP3

Gwamnan ya nuna jajirce wa wajen saka ilimi a gaba.

Ya Kuma bayyana cewa za a bude jami’u 20 wanda gwamnatin da ta gabata ta kulle.

DOWNLOAD ZIP

Yusuf ya godewa masarautan da yaba musu wajen tabbatar da zaman lafiya, wanda hakan ya yiwu ne domin daukaka Al’ada da Kuma cigaban jiha.

Rushe Rushe: Haryanzu Banyi Da Na Sani Ba In Ji Gwamnan Kano

 

Mai Martaba Bayero ya yi kira ga gwamnati da ta kawo taki wa mutanen kano a farashi mai sauki, dawo da campaign din shuka itatuwa da ruwa a jihar Kano.

Ya Kuma yi kira ga gwamnatin jiha da ta kawo sarari a jihar yanda zai saka mutane su yunkuro dan saka hannun jari a jihar dan samun cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button