Labaran YauPolitics

Shugaban Kasa Meh Jiran gado Tinubu na bukatan Addu’o’i inji Masari

Shugaban Kasa Meh Jiran gado Tinubu na bukatan Addu’o’i inji Masari

Mai girma gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari, Yace, shugaban kasa meh jiran gado Bola Ahmed Tinubu yana bukatar addua daga yan kasa Najeriya dan ya samu ya gudanar da mulkinsa dan cimma nasara wa kasa baki daya.

Masari ya bayyana hakan ne a wajen buda baki da Aka shirya a gidan gwamnatin katsina ran laraba dan karya azumi.

A fadin shi gwamna, shi shugaban kasa meh jiran gado ya saba da shirya irin wannan taro shan ruwa a kowata mako na ramadana dan yin addu’o’i.

Wannan shekaran ta musamman aka shirya ne dan godiya wa Allah na samun nasara a zaben da ta gabata a wannan kasar.

Ya ce, ba wani abu da zasuyi in Banda godewa Allah dan samun Nasara a katsina da Kuma kasar mu Najeriya.

Shine makasudin haduwan mu gaba daya, da shuwagabanni na mu na addini da gargajiya da Kuma na gwamnati da dattijan jiha baki daya.

Bola Tinubu shine sabon shugaban kasan Najeriya Kuma yana bukatan adduan mu. Kuma mutane sun fahimci hakan bayan zaban shi Kuma addua itace ake bukata. Inji Masari.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button