Labaran Yau

Sanusi Yayi Shigar Sarauta A Wata Shagali A Legas Bayan Maganan Dawowar Shi Kujerar Sarauta

Sanusi yayi shigar Sarauta a wata shagali a legas bayan maganan dawowar shi kujerar Sarauta

Alhaji Muhammadu Sanusi,Sarki na goma sha hudu na Kano, ya zama abun kallo a wajen shagalin cin abinci a legas ranan Asabar.

Sanusi ya kasance babban bako a wannan taron da Herbert Wigwe Shugaban bankin AccessBank na Najeriya hada.

Muhammadu II ya halarci taron awanni bayan Kwankwaso ya fadi cewa zasuyi duba da dalilan da yasa aka cire shi a sarautar Kano.

Sanusi yazama sarki a karshen tenuwan kwankwaso na gwamnan Kano , wanda gwamna Mai fita Abdullahi Ganduje ya cire shi wanda shine mataimakin gwamna a a lokacin da ya zama sarkin Kano.

An cire Sanusi ran tara da wayan maris shekarar 2020, Kuma aka koreshi zuwa garin Loko da Awe a jihar Nasarawa. Kuma duka kudaden da ya kashe anyi bincike akai.

Ganduje ya Kuma raba masarautar zuwa kashi biyar, ya Kuma bada Sarautar wa wanda basu Abota.

Kwankwaso yace Munyi kampen kuma ansan yanda muka sanu a jihar Kano da Najeriya. Zamu cigaba da aikin mu masu kyau daga inda muka tsaya. Wannan sabon gwamna da mukarrabansa zasuyi abinda ya dace”

“ A matsayin mu na manya, Zamu cigaba da basu shawarwari suyi abinda ya dace, bamuyi kokarin cire wani ko hana cire wani ba, amma yanzu dama ta samu.

“Wanda aka basu daman zasu zauna Kuma sugani yadda zata kasance, kuma abinda ya kamata suyi. Shi sarkin da masarautar an raba ta kashi biyar. Shugaba yakan gaji Mai kyau, Mara kyau da wasu lamari wanda ke da wuyan gyarawa”.

Ya Kuma roki Allah da ya taimaka musu da sabon gwamna wajen yin abinda ya dace cikin sauki.

Ga hutunan Sanusi a wajen taron Shagalin:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button