Labaran Yau

Tsofaffin Kwamishinoni Guda 2 Sun Rasu Cikin Kwana 3 A Jihar Kano

Tsofaffin Kwamishinoni Guda 2 Sun Rasu Cikin Kwana 3 A Jihar Kano

Jihar Kano ta yi rashin tsofaffin kwamishinoni biyu da suka yi aiki karkashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau.

Tsofaffin kwamishinonin da suka rasa rayukan su, akwai Alhassan Muhammad Dawaki wanda ya yi aiki a karkashin tsohon gwamna Shekarau yayin da Barista Zubaida Damakka ta yi aiki a karkashin tsohon gwamna Ganduje.

Dawaki ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya yana da shekaru 79 kuma ya bar mata da ‘ya’ya 15.

Wani na hannun damar marigayi Damakka wanda tsohon babban mataimaki na musamman ga gwamna kan kafafen sadarwa na zamani, Abubakar Aminu Ibrahim ya tabbatar da rasuwar ta, inda ya ce ta rasu ne a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya, ta bar ‘ya’ya uku da miji.

An yi Sallar Jana’izar su a Kano ranar Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, ya bayyana Dawaki a matsayin fitaccen mutumi kuma mutum ne mai mutunci wanda rasuwar tasa babban rashi ga al`ummar jihar ta kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na’am da gagarumin rashi da rasuwar Dawaki ta yi a lokacin da yake gabatar da addu’o’in samun karfin gwuiwa da juriya ga ‘yan uwa da ke cikin makoki, yana mai yi musu fatan Alheri a cikin mawuyacin hali na makoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button