Garuruwan Malam Fatori da ke makwabtaka da Najeriya da kuma Bosso a Nijar, wadanda a baya kan samu alaka ta sada zumunta ta yau da kullun tsakanin sojojin Najeriya da sojojin jamhuriyar Nijar a Bosso, yanzu haka suna fuskantar tashin hankali da rashin jituwa saboda abubuwan da suka faru a baya-bayan nan na rashin dai daito tsakanin sojojin da suka karbi mulkin Nijar da kuma gwamnatin Najeriya.
Biyo bayan takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa kasar da kuma ayyana yiwuwar daukar matakin soji, Najeriya da Nijar sun shiga tsaka mai wuya.
Hakan ya sa sojojin Najeriya ke fuskantar koma baya inda aka hana su shiga garin na Bosso domin samun kayayyakin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum da kuma sauran ababen more rayuwa.