Labaran Yau

Likitoci Sun Bawa Gwamnati Sati Biyu Dan Karin Albashin Su

Likitoci sun bawa Gwamnati Sati biyu dan karin Albashin su

Kungiyar likitocin Najeriya sun bada sati biyu wa gwamnatin tarayya dan ta kara musu albashi.

Ita kungiyar ta bayyana hakan ne bayan zaman da tayi na Majalisan likitocin kasa da akayi a garin Abeokuta na jihar Ogun.

Bayanin ya bayyana wa Hukumar labarai ta kasa da saka hannun Shugaban su, dakta Innocent Orji, sakatare janar dakta kelechi chikezie, da sakataren sadarwa dakta Musa Umar.

Sunce suna bukatan karin albashi kashi dari biyu bisa dari da Kuma sabon tsari na Alawus a takardadan da suka turawa ministan lafiya a shekarar 2022 dan dubawa.

A bayanin kungiyar, duba da yanda gwamnati take tsare tsare wanda zata duba ta gyara musu Albashin, babu canji tunda aka yi a shekara goma da ta gabata.

“Gwamnati bata taba kiran kungiyar ba dan zama ayi gyaran albashin su ba.

“Kuma bata yi duba da canjin rayuwa da kasa take fuskanta ba, duba da tsadar rayuwa, faduwar naira, da Kuma hazaka wajen cire tallafi a kasan.

“Sun bada lokacin da gwamnati zata kara musu kudade”.

Duk da an kawo tsarin karin Albashi bayan duk shekara biyar a shekarar 2014, ba a taba karawa ba. Bayan an aminta da hakan tun 2009.

Sati biyun da suka bada zai fara ran 29 ga watan Aprailu a gama ran sha uku ga watan mayu, in hakan bai yiwu ba bare sa mu samu hadin kai da gwamnati ba.

Kungiyar sun tunatar da a basu kudin MRTF na shekarar 2023, wanda akayi yarjejeniyar da ministan lafiya.

Sun bukaci a biyasu cikon kudin albashinsu na 2014, 2015 da 2016, da Kuma daidai ta karin kudin albashi da akayi.

Kuma sun ja kunne kan yadda gwamnoni ke iya barci bayan rashin kula da lafiyan mutane.

Akan lasisin aikin likita bayan yin aiki na shekara biyar da Majalisan tarayya ta kawo. Sunce barasu lamunta ba. Dan dokar zata mai da likitocin bayi ne.

Kuma sun nemi a dauki aiki a asibitocin da karancin ma’aikatan, Kuma ayi gyaran asibitocin dan inganta aikin jami’an lafiya da Kuma samun lafiyan mutane.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button