Sojoji Sun Hargitsa Mazaunin `Yan Ta’adda Tare Da Hallaka Wasu A Garurruwan Sokoto Da Zamfara
A kokarinsu na ci gaba da samun nasarorin baya-bayan nan da sojoji suka samu a yankin Arewa maso Yamma, dakarun Operation Hadarin Daji a jihar Zamfara a ranar Juma’a sun kara kaiwa mazaunan `yan ta`adda fatattaka.
A cikin ayyukan hadin gwiwa na baya-bayan nan, sojojin sun fatattaki sansanonin ‘yan bindiga a kauyukan Mutuwa, Guda Tudu, Kawar, Dantayawa, Gidan Kare, Mahuta, da Gyado na jihohin Zamfara da Sokoto.
Wata majiya mai karfi da ta so a sakaya sunanta ta shaidawa jami`an mu cewa, a yayin gudanar da aikin, sojojin da suka tunkari gungun ‘yan bindigar da karfin tsiya, sun tsorata ‘yan fashin yayin da gaba daya suka gudu daga yankunansu kafin isowar sojojin.
Sai dai sojojin sun kwato babura guda hudu na ‘yan bindigar inda nan take sojojin suka lalata sabon mazaunin da `yan fashin suka kafa.
Hakazalika, dakarun Operation Hadarin daji da aka tura a Forward Operating Base (FOB) Faru, a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun samu sahihan bayanai kan aniyar ‘yan bindigar na kai hari kauyen Bagabuzu, wanda sojojin suka dakile shi ta hanyar ragargazar mazaunan `yan ta`addan da ke wadannan shirye shirye.
Dakarun sojojin sun yi gaggawar zuwa yankin gaba daya, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi, suka hana su shiga kauyukan.
Bayan arangamar dai an kashe ‘yan bindiga hudu yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga a jikin su.
Yayin da suke dakile harin, sojojin sun kwato bindiga kirar Janaral Purpose Machine (GPMG) guda daya, bindigar FN daya, da harsashi na musamman guda 123.
A halin da ake ciki, Babban Kwamandan Runduna ta 8 Sokoto/Kwamandan Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yabawa sojojin bisa jajircewarsu, da jajircewa da kuma ciyar da ‘yan ta’addan yaji da barkono.
Ya yi kira ga jama’a da su tallafa wa sojojin da sahihan bayanai game da ayyukan ‘yan bindiga domin daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.