Labaran Yau

Tsohon Kwamishinan El’Rufai Ya Wallafa Littafi Kasar Jamus

Tsohon Kwamishinan El’Rufai Ya Wallafa Littafi Kasar Jamus

Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo) tsohon kwamishina na kasafi da tsare tsare karkashin Gwamnatin Tsohon Gwamna Nasiru Ahmed Elrufai na jihar kaduna.

Ya wallafa littafi mai peji 255, wanda ya kira Rugujewa; Sabon tunani na mulki wanda zai kawo sauki wa talata (Disruption: Rethinking Governance to work for the poor).

Littafin an wallafa shi a birnin Berlin na kasar Jamus, a kampanin wallafa ta Almara, jagoran wallafan Hadiza Ismail Elrufai matan tsohon gwamnan Kaduna.

Gabatarwan Amina J Mohammed, maitaimakiyar Sakatare janar na Majalisan dinkin duniya.

A bayanin Ahmed Maiyaki, wanda ya kula da kafafafen Sadarwa da zantarwa na taron ya bada bayani akan taron.

A bayanin maiyaki, Littafin ta tsunduma cikin binciken samo manyan lamuran da suka tunzura kirkiro gwamnatin da ta fi saka Ido kan talakawa da wanda basu da galiho a wuraren mu.

Yace littafin tazo ta kawo canji Mai ma’ana da Kuma tunani na zamani wajen magance matsalolin yau ta hanyar amfani da hanyoyin Zamani.

Mawallafin littafin ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu wajen daukan matakin cire tallafin man fetur, yace tallafin mai ta amfanu mutum kalilan ne a cikin yan Najeriya da hannun wasu batattun yan siyasa akan yawan mutanen kasa.

Dattijo

Dattijo ya nuna cewa amfani da kudaden tallin za ayi wajen kula da tsaron dan kasa saboda rashin yarda wanda ya jima tsakanin dan kasa da gwamnati.

Ya kara da cewa dan bunkasa kasuwanci Sai an daukaka samun talaka dan kasuwa tayi inganci.

A wajen wallafan littafin, Ambasadan Najeriya a jamus, Yusuf Tuggar, ya yabawa mawallafin na zaman sa A Majalisan dinkin duniya da tunanin shi na komawa Najeriya dan yayi aiki wa kasa karkashin Elrufai.

Tuggar ya bada karfin gwiwa wa Najeriya da kasashen duniya da suyi amfani da sabuwar hanya na littafin, wanda ta magance matsaloli na gudanar wan gwamnati a sabuwar tunani na Zamani dan samun cigaban kasa dan kasa.

Wallafan littafin ta hada baki kala kala, sun hada da jami’un diplomashiya, jiga jigan jamus, EU, jami’un gwamnatin jamus, kungiyoyin Sibil society da yan ilimi.

Wata wallafan da za ayi a Najeriya, kaduna Abuja da legas inda za ayi wallafa da karanta littafin a watan yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button